Yadda masu fisge ke addabar mazauna unguwar Mararraba a Abuja

Mazauna garin Mararraba da ke kusa da babban birnin tarayya Abuja a Najeriya na kokawa bisa ƙaruwar masu fisge wayoyi da jakunkuna da ma sauran kayayyakin al'umma.
Mararraba yanki ne da ke karkashin jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, amma akasarin mazauna garin mutane ne da ke aiki a ƙwaryar birnin tarayya Abuja, sai kuma masu zuwa ci rani daga sassan kasar daban-daban.
Wannan ne ma ya sa ake yi wa garin laƙabi da sabuwar Legas.
Akwai wurare da dama da 'yan fisgen suka fi yin aika-aikarsu.
Daya daga cikin wadannan wuraren su ne Kwanar Aso, inda idan karfe 6 zuwa 7 na maraice ya yi dole matafiyi ya yi taka tsan-tsan idan ba haka ba kuwa zai tafka asara.
Masu irin wadannan ayyukan na amfani ne da kananan makamai kamar wuƙaƙe da adduna da dai sauran su wajen far wa al'umma, domin ƙwace wayoyi da jakunkuna da sauran kayayyaki.
Unguwar na da mutukar girma, kuma wasu gidajen da ke yankin ba sa cikin tsarin hukumomin tsara birane.
Har ila yau, unguwar ta kasance matattarar mutane daban-daban. Wasu da ke aikata laifuka iri-iri a sassan Najeriya na mayar da Mararrabar wurin ɓuya.
Koke-koken da mutane ke yi
Mararraba unguwa ce da ta haa mutane daga sassan asar daban-daban

Mr. Wislon wani dan kasuwa da ke sana'ar POS ne, wato karbar kudi da aikawa ta hanyar amfani da nau'ra, kuma ya taba fadawa hannun masu fisgen.
Ya ce ya shiga abin hawa na Adaidaita Sahu ne tare da su bisa rashin sani, sannan suka wafce masa 'yan kuɗaɗensa.
"Gungun ɓarayi ne wanda ba za ka sani ba, mun fara tafiya sai suka fitar da adda suka sare ni a kai, kafin kace kwabo sun ƙwace kudin da ke hannuna har naira dubu dari biyu da hamsin, na yi ta ihu amma babu wanda ya kawo min ɗauki".
Shi ma Mr. Jerry wani dan unguwar ta Mararraba ne da ya taɓa fadawa hannun masu fisgen ya ce babu wanda zai tsira sai wanda Allah ya tserar.
"Abun ya wuce gona da iri, domin kullum sace-sace karuwa suke yi, hakan na faruwa ne sakamakon rashin aiki da kuma yawan shaye-shaye," in ji Mr. Jerry.
Tattaunawa da shugaban 'yan fisge

Bayan sauraron koke-koken wadanda suka fada tarkon barayin, BBC ta zanta da mutumin da ke shugabantar gungun 'yan fisge a yankin na Mararraba wanda ake yi wa laƙabi da Oga Boss.
"Muna ƙwace wayoyi a hannun jama'a a wasu lokutan ma idan abin ya gagara mukan yi amfani da wuƙa wajen yanke mutum domin samun damar ƙwace waya, bayan mun ƙwace ne muke samun na shaye-shaye."
Shugaban ɓarayin ya ƙara da cewa shi dan asalin jihar Gombe ne, kuma daga can ya tafi Legas sannan ya koma Mararraba yanzu.
"Da can a Gombe nake da zama sai na sare ƙafar wani a can, daga nan aka fara nema na sai gudu Legas, amma bata yi daɗi ba daga nan na dawo Mararraba."
A cikin gidan na Oga Boss akwai yara ƙanana ƴan kimanin shekara 12 zuwa 15, kuma ya ce sabbin yaran gidansa ne.
"Yaran dai marayu ne ba su da iyaye, shi ya sa muka tattaro su domin koya musu sana'ar sace-sace har ma da yankan aljihu, don su ma su sami abin yi," in ji shi.
Me rundunar ƴan sanda ke yi a kan lamarin?
Rundunar 'yan sanda a jihar Nasarawa wacce unguwar Mararraba ke ƙarƙashinta ta ce ta ɓullo da sabbin dabarun magance matsalar fisge da ke ci wa mutane a yankin tuwo a ƙwarya.
Kakakin rundunar ASP Ranham Nansel ya ce ƴan sanda sun yi sabbin kame.
"Yanzu haka da nake magana da kai na ga shigowar wani rahoto da ke nuna cewa an kama takwas daga cikin masu fisgen, an kuma gurfanar da su gaban kotu," in ji ASP Ranham Nansel.
Ya ƙara da cewa an zaɓi wuraren da abubuwan nan ke faruwa an kai ƙarin jami'an tsaro domin magance matsalar.











