Yadda 'ƙwacen waya da fashi da makami ya zama ruwan dare a Kano'

Dabi'ar ƙwacen waya da lalata ababen hawa da faɗace-faɗacen daba da kuma fashi da makami na ci gaba da ƙamari a Kano.
A wasu lokutan dai matasa kan yi amfani da taruka kamar na siyasa ko na biki ko kuma idan an samu cunkoso a kan tituna sai su yi amfani da makami kamar wuƙa wajen yi wa mutane ƙwace.
Irin waɗannan matasa kan fito da makami su yi wa mutum barazana a kan idan har bai ba su abin da suka buƙata ba sai su ji masa rauni, idan ya zo da ƙarar kwana ma a kan rasa rai.
Matasan da ke wannan ɗabi'ar dai ba su ƙyale mata ba ma, ba wanda ba sa yi wa ƙwace musamman ma na wayar salula.
Al'ummar jihar Kano sun ce wannan al'amari da yanzu ya zama ruwan dare game duniya sai dai addu'a kawai.
Wata mata da aka yi wa irin wannan ƙwacen da ta nemi a sakaya sunanta a Kanon, ta shaida wa BBC cewa wannan ɗabi'a ta yi yawa.
Ta ce "Rannan na dawo daga gidan biki ga ni ga gida ma ina kallo sai wasu samari biyu suka tare ni, ina ji ina gani ina son wayata haka na haƙura da ita na ba su, don har yankata suka yi a hannu".
Shi ma wani da irin haka ta faru da makwabcinsa ya shaida wa BBC cewa, abokin nasa tela ne ya tsaya a wuraren unguwar Court Road yana jiran a dai-daita sahu sai ga wasu maza su biyu suka zare ƙaho suka ce ko ya ba da waya ko kuma su ɓurma masa ƙahon nan.
Ya ce maƙwabcin nasa bai musa ba ya ɗauki waya ya ba su su kuma suka wuce suka tafi abinsu maganar sai dai a labari.
Wasu daga cikin mazauna birnin na Kano sun ce irin wannan ƙwace na waya ba wai na kan hanya kawai ake yi wa ba, a kan je har gida a yi sallama da mutum sannan a nemi ya bayar da wayarsa idan bai bayar ba sai a sa masa makami.
Duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi a jihar wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, wannan matsala ta ƙwacen waya ko fashi da makami na ci gaba da yaɗuwa.
To sai dai kuma a nasa ɓangaren mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Kano, DSP Abdullahi Haruna Kyawa, ya ce an samu ragin aikata irin waɗannan ɗabi'u.
DSP Abdullahi, ya ce suna kama masu aikata laifuka da dama, kuma ba za su yi ƙasa a gwiwa ba za su ci gaba da kama irin waɗannan mutane.
Fatan al'ummar jihar ta Kano shi ne, gwamnatin jihar ta cika alkawarin da ta yi na sanya na'urar naɗar hotuna a manyan titunan jihar da kuma inda ake samun hada-hadar al'umma domin zaƙulo irin waɗannan ɓata gari a cikin al'umma.











