Hotunan yadda shugabannin ƙungiyar G7 suka shakata a taron Cornwall

Taron ƙoli na ƙungiyar G7 a yankin shakatawa na Carbis Bay da ke Cornwall a kudu maso yammacin Ingila, inda shugabannin Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da Amurka da kuma Birtaniya sun hallara a wuri guda a karon farko.

Ga wasu hotunan shugabannin daga wurin taron.

Carrie Johnson with Wilfred Johnson as Kim Jung-Sook, Jill Biden, Brigitte Macron look on

Asalin hoton, Simon Dawson/No 10

Bayanan hoto, A rana ta biyu ta taron ƙolin ƙungiyar G7 ran Asabar, an yi taron a yanayi mai dumi da hasken rana - kuma shugabannin sun shakata a kusa da gabar teku. Firaministan Birtaniya Boris da mai ɗakinsa Carrie sun nuna wa baƙin nasu Wilfred, ɗan su mai shekara ɗaya..
G7 leaders watch the Red Arrows display

Asalin hoton, Andrew Parsons/No 10

Bayanan hoto, Shugabannin na G7 na kallon wasa na musamman da rundunar sojin sama ta RAF Red Arrows ta gabatar.
Red Arrows flying over Carbis Bay, Cornwall

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazauna yankin na Cornwall ma sun taru domin kallon wasan da jiragen yaƙin suka yi.
Joe Biden and First Lady Jill Biden with the Queen

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Bayan ya bar Cornwall, Shugaban Amurka Joe Biden tare da mai ɗakinsa Jill Biden sun kai wa Sarauniyar Ingila ziyara ta musamman a Fadar Windsor Castle.
Boris Johnson goes for a swim on Sunday morning
Bayanan hoto, Firaministan Birtaniya ya farka da wuri ranar Lahadi domin yin ninƙaya a teku gabanin a fara taron wannan yinin.
Boris and Carrie Johnson on beach at Carbis Bay
Bayanan hoto, Mai ɗakin Firaministan, Carrie ta tarbi mijin nata bayan ya kammala wanka a cikin teku.
Emmanuel Macron and Boris Johnson chat with Red Arrows official at G7 summit

Asalin hoton, Andrew Parsons/No 10

Bayanan hoto, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Boris Johnson na tattaunawa a wani wurin da aka shirya musu tsire a gabar tekun Cornwall.
Prime Ministers wife Carrie Johnson walks with US First Lady Dr Jill Biden at the Minack Theatre

Asalin hoton, Simon Dawson/No 10

Bayanan hoto, Carrie Johnson da mai ɗalin Shugaban Amurka Jill Biden sun ziyarci gidan wasan kwaikwayo na Minack Theatre da ke da duwatsu masu ƙayatarwa a Porthcurno.
Prime Minister Boris Johnson greet France's President Emmanuel Macron with an elbow bump as their spouses look on in Cornwall, during the G7 summit

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mista Johnson na gaisuwar korona da Mista Macron yayin da matansu - Carrie Johnson (a dama) da Brigitte Macron (a hagu), ke kallonsu.
From left, President of the European Commission Ursula von der Leyen, Germany's Chancellor Angela Merkel, Japan's Prime Minister Yoshihide Suga, France's President Emmanuel Macron, Canada's Prime Minister Justin Trudeau, Britain's Prime Minister Boris Johnson, Italy's Prime minister Mario Draghi, President of the European Council Charles Michel, and US President Joe Biden during an evening reception at The Eden Project

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugabannin sun hallara a wani biki mai suna Eden Project da Sarauniyar Ingila ta shirya da yammacin Juma'a.
The Prime Minister Boris Johnson and his wife Carrie meet the US President Joe Biden and the First Lady Jill Biden in Carbis Bay Cornwall ahead of the G7 Summit

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Boris Johnson da mai ɗakinsa Carrie sun gana da Shugaban Amurka Joe Biden da mai ɗakinsa Jill Biden.
Police officers are seen on a rigid inflatable boat in St Ives in the sea

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Daya daga cikin kwale-kwalen da jami'an tsaro su ka yi amfani da shi a gabar tekun Cornwall domin samar wa shugabannin na G7 yanayin da ya dace su tattauna cikin natsuwa.
A baker puts a pasty in his shop window with G7 marked in pastry

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Wani gidan biredi a Cornwall ya samar da wata cimaka ta musamman mai suna pasties da alamar G7 a jiki.
The Duchess of Cambridge and First Lady Jill Biden visit a school

Asalin hoton, Aaron Chown / PA Media

Bayanan hoto, Duchess of Cambridge, tare da Jill Biden, na kallon ayyukan da ɗaliban wata makaranta mai suna Connor Downs Academy da ke Hayle, a yammacin Cornwall.
Carrie Johnson with Jill Biden and Wilfred Johnson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mrs Biden da Mrs Johnson sun cire takalmansu domin shaƙatawa a gabar tekun Carbis Bay, a daidai lokacin da Wilfred Johnson - ɗan Firaminista Boris Johnson - ke kallonsu.
Street in Cornwall

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda 'yan sandan Birtaniya su ka samar da tsaro. Nan ana iya ganin wani shago da aka ƙayata da tutocin ƙasashen ƙungiyar ta G7 yayin da shugabannin ke barin Tregenna Castle a Carbis Bay.

Dukkan hotunan nan akwai haƙƙin mallaka a kansu.