Taron ƙolin G7: Ƙungiyar ta ware kuɗaɗe domin tunkarar China

G7 leaders meeting in Carbis Bay, Cornwall (11 June)

Asalin hoton, Leon Neal/PA Media

Shugabannin Ƙungiyar G7 ta manyan ƙasashe mafi ƙarfin tattalin arziki sun samar da wani sabon shiri da a ƙarƙashinsa za su taimaka wa ƙananan ƙasashe ta hanyar samar da kayayn raya ƙasa.

Shugaba Joe Biden ya ce yana son ganin wani shirin da Amurka ta samar mai suna "Build Back Better World" (wato B3W) ya kasance ya zarce wanda China ke samar wa.

Shirin da ya ke nufi shi ne Belt and Road Initiative (BRI) wanda a ƙarƙashinsa ta ke gina hanyoyin mota da na jirgin ƙasa da tashoshin jiragen ruwa a ƙasashe masu dama.

Sai dai ana kushe shirin saboda yana tara wa ƙasashen ɗumbin bashi.

A wata sanarwa da shugabannin su ka fitar yayin taron ƙolin da su ke yi a yankin Cornwall na ƙasar Ingila, shugabannin G7 ɗin sun ce za su samra da wani tsari da ƙawancen da aka gina bisa "turbar amincewa da juna".

Sai dai ba a san ainihin abin da wannan shirin ya ƙunsa ba. Shugabar Jamus Angela Merkel ta ce ƙungiyar ba ta kai matsakin da za fitar da yawan kuɗaɗen da za ta samar wa shirin nata ba.

Workers walk by the perimeter fence of what is officially known as a vocational skills education centre in Dabancheng in Xinjiang Uighur Autonomous Region, China September 4, 2018.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, China ta ƙirƙiri wasu maka-makan sansanoni a yankin Xinjiang na ƴan ƙabilar Uighur

Amurka ta daɗe tana sukar shirin China wanda ta ke kira "diflomasiyyar bashi."

Ƙungiyar ta G7 ta kuma ce za ta samar da wani tsarin da zai kawo ƙarshen cutututtuka masu yaduwa da ke haddasa annoba a shekaru masu zuwa.

Firaministan BIrtaniya Boris Johnson ne mai karɓar baƙuncin sauran shugabannin da ke halartar taron ƙolin a wani wurin shakatawa da ke gaɓar teku mai suna Carbis Bay.