John Magufuli: Shugaban Tanzania ya mutu bayan an yi rade radin ya kamu da korona

John Pombe Magufuli

Asalin hoton, Getty Images

Shugaban Tanzania John Pombe Magufuli ya mutu.

Mataimakiyar Shugaban ƙasar Samia Suluhu ce ta tabbatar da mutuwar shugaban a kafar yaɗa labaran ƙasar.

A cewar mataimakiyar shugaban, Mista Magufuli ya mutu ne da yammacin ranar Laraba a asibitin Mzena da ke Dar es Salaam sakamakon ciwon zuciya.

Ya shafe fiye da shekara 10 yana fama da larurar. Saluhu ta ƙara da cewa a ranar 14 ga watan Maris ne jikin shugaban ya yi tsanani inda kuma aka kwantar da shi a asibiti - a nan kuma ya mutu.

Ya mutu ne yana da shekara 61 da haihuwa.

John Pombe Magufuli, ɗan wani manomi ne da ya zama shugaban ƙasa a 2015. Ya zama shugaba mai yawan janyo cece-kuce musamman kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da batun annobar korona.

An zaɓe shi a wa'adi na biyu a shekarar 2020 duk da zarge-zargen da bangaren hamayya ya yi na cewa an tafka maguɗi a zaben.

Kafin ya zama shugaban kasa aka ba shi lakabin "the bulldozer" saboda yadda ya jagoranci aikin samar da tituna a matsayinsa na ministan ayyuka daga bisani kuma aka yaba masa saboda jajircewarsa wajen yaki da cin hanci da barnatar da kudi.

line

Yadda Magufuli ya kalli annobar korona

A lokacin da annobar korona ta ɓulla a Tanzania, Shugaba Magufuli bai yadda da mutane su zauna a gida ba. Yana so su koma masallatai da coci-coci domin gudanar da addu'o'i.

"Cutar korona wadda sheɗaniya ce ba za ta rayu a jikin mabiyan Yesu ba, za ta ƙone nan take", in ji Magufuli, wanda Kirista ne kuma ya ayyana hakan a ranar 22 ga watan Maris na 2020 a Dodoma babban birnin ƙasar.

Shugaban ya ce ba zai tsayar da harkokin kasuwancin ƙasar ba, duk da cewa wasu na sukar hanyar da ya bi ta shawo kan annobar.

line

Wane ne John Magufuli?

John Pombe Magufuli

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Magufuli ya zama shugaban kasa a 2015
  • An haife shi a Chato, arewa maso yammacin Tanzania a 1959
  • Ya yi karatu a fannin ilimin sinadarai da lissafi a Jami'ar Dar es Salaam
  • Ya koyar a matsayin malamin chemistry da lissafi
  • An zabe shi a matsayin dan majalisa a 1995
  • Ya zama mamba a majalisar ministoci a 2000
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2015
  • A 2020 ne kuma aka kara zabensa karo na biyu

Muhawara kan ayyukansa

Sharhi daga Dickens Olewe, BBC News

John Magufuli ya kasance shugaban kasa da ke da kazar-kazar, abin da ya saba da tsarin magabacinsa.

Tsarin shugabancinsa na saukin kai ya sa ya samu magoya baya daga Tanzania, da ma wasu kasashen Gabashin Afirka inda aka kirkiri maudu'i mai taken #WhatWouldMagufuliDo wato #MaiMagufuliZaiYi a shafin Twitter saboda tsarinsa na yaki da cin hanci.

Za a yi muhawara sosai game da ayyukan da ya yi da kuma ko wadda za ta gaje shi za ta ci gaba da tsare-tsarensa ko kuma za ta sauya alaka.

Sai dai ba za a daina tattaunawa kan irin wadannan batutuwa ba a nahiyar Afiirka inda fafutukar mulkin dimokradiyya ke ci gaba da samun wurin zama kodayake galibin mutane ba sa jin dadi game da rashin cika alkawuran shugabanni na samar musu abubuwan more rayuwa.

Don haka duk da yake 'yan Afirka da dama za su so samun shugaba mai kazar-kazar irin Magufuli, kazalika suna son samun shugabanni masu gaskiya da kuma gwamnati da take mutunta su wadda ba ta boye bayanai game da lafiyar shugabanta.

An alakanta mutuwar Magufuli da ciwon zuciya da ya dade yana fama da shi, amma da dama daga cikinsu suna zargin cewa ya mutu ne sakamakon kamuwa da Covid-19.