Magufuli ya lashe zaɓen Tanzaniya duk da korafin aringizo

John Pombe Magufuli

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar zaɓen Tanzaniya ta ayyana shugaban John Pombe Magufuli a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar Laraba.

Hukumar ta ce shugaban ya lashe zaɓen ne da kuri'a miliyan 12.5 cikin kuri'a miliyan 15.9 da aka kaɗa.

Babban abokin hamayyar Mr Magafuli, Tundu Lissu, ya ce an hana wakilan jam'iyyarsu shiga wuraren zaɓe a ranar zaɓen, abin da hukumar zaɓen ƙasar ta yi watsi da zargin nasa.

Shugaba Magafuli dai ya samu kaso 84 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Mr Lissu ya samu kaso 13 cikin 100 na kuri'un.

Ɗaya daga cikin masu sanya idanu a zaɓen da ya zo ƙasar ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana ba tare da hargitsi ba.

Tun da farko Mr Lissu na jam'iyyar Chadema, ya ce ba zai amince da sakamakon zaɓen ba yana mai cewa ba zaɓe aka yi ba domin an saɓa dokokin zaɓe.

Ya ce,"Wasu gungun mutane ne suka yanke shawarar amfani da ɓata gari domin su cimma manufarsu ta ɗarewa mulkin ƙasa".

Ya kuma yi zargin cewa an yi aringizo a cikin akwatunan zaɓen a lokacin da wakilan jam'iyyarsu ba sa wajen.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Dar es Salaam, ya ce bisa la'akari da yadda zaɓen ya gudana har shugaba Magafuli ya samu nasara akwai shakku a cikin sakamakon, da kuma nuna damuwa a kan makomar dimokradiiya a ƙasar.

Tuni dai shugaban hukumar zaɓe Semistocles Kaijage, ya ce dukkan zarge-zargen da ake na cewa an yi amfani da takardun kada kuri'a na bogi duk ba gaskiya bane.