Shugaban Tanzania na son malamai su zane dalibansu

Tanzania
Bayanan hoto, Hoton da ya yi ta zagaya kafafen sada zumunta inda malami yake zabaga wa dalibai bulala

Shugaban Tanzania John Magufuli ya yi kira da a samar da sauyi dangane da dokar horar da dalibai ta hanyar yi musu bulala.

A yanzu dai dokar ta yi iyaka, don haka shugabannin makarantu ne kadai ke da damar zane dalibansu, amma a yanzu shugaban na neman bai wa kowane malami damar zane dalibinsa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Shugaban na magana ne bayan wani faifan bidiyo da ya yi ta zagayawa a shafukan sada zumunta, da ya nuna wani kwamishinan yanki da ya yi ta tsala wa dalibin wata makarantar kwana bulala saboda zargin cinna wa dakin kwanansu wuta.

Mutane da dama sun caccake shi, toh amma shugaba Mugufuli ya fito karara ya ce ya yi magana da shi, kuma ya karfafa masa guiwar cigaba da yin hakan.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam a kasar sun ce laifukan take hakkin dan adam a Tanzania sun karu tun bayan darewar shugaba Mugufuli kan karagar mulki a shekarar 2015.