Amazon da Reliance: Abin da ya haɗa masu arziƙin duniya biyu faɗa har da zuwa kotu

Jeff Bezos speaking

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu sharhi sun ce Amazon bai taɓa samun kansa a gasar yin fice ba irin wannan karon da yake gwabzawa da Reliance

Wata rigima kan wani shagon sayar da kayan masarufi ta sa babban kamfanin nan na duniya Amzon yana faɗa da kamfani mafi girma a Indiya wato Reliance.

Kamfanonin suna rikici da juna ne saboda dukkan su sun shiga wata yarjejeniya da wani kamfani na Indiya mai suna Future Group.

Msu sharhi sun ce rikicin da ake yi a kotun, inda kamfanin Amazon da ke Amurka yake ƙalubalantar kamfanin Indiya a ƙasarsa, ka iya yin tasiri sosai a haɓakar kasuwancin intanet a Indiya nan da shekaru masu zuwa.

"Ina ga wannan babban abu ne. Amazon bai taɓa ganin irin wannan adawa a dukkan kasuwancinsa ba," kamar yadda Satish Meena, wani babban mai sharhi daga kamfanin Forrester ya shaida wa BBC.

Kamfanin Amazon ya sa shugabansa ya zamo wanda ya fi kowa kuɗi a duniya (duk da cewa a yanzu wani ya fi shi) sannan kamfanin ya sauya yadda ake sayen kaya ɗa-ɗai a duniya. Amma shugaban kamfanin Reliance Mukesh Ambani - wanda shi ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a duniya - yana da tarihin yawan shiga rikici.

Masu sharhi kan masana'antu ya ce shirye-shireyensa kan fara kasuwancin sayar da kaya ɗai-ɗai zai zama babban ƙalubale ga Amazon, da kuma kamfanin Flipkart mamallakin Walmart.

Amazon ya daɗe yana faɗaɗa kasuwancinsa da gasken-gaske a Indiya, inda yake fatan cin gajiyar kasuwancin intanet. Shi ma kamfanin Reliance ya yi shirin faɗaɗa kasuwancinsa na intanet da kuma na kayan masarufi.

Me ya haɗa faɗan da ake yi a kan kamfanin Future Group?

A farkon shekarar nan ne kamfanin Future Group ya ƙulla yarjejeniyar sayar wa da Masana'antu Reliance ƙadarori da kuɗinsu ya kai kimanin dala biliyan 3.4.

Tun shekarar 2019, Amazon ya mallaki kashi 49 cikin 100 na hannun jarin kamfanin Future, wanda hakan ya ba shi dama a fakaice ta mallakar wani kaso na kasuwancin ɗai-ɗai na kamfanin Future.

Amazon ya ce a yarjejeniyar wannan ciniki, Kamfanin Future ba zai iya sayar da kaya ga wasu zaɓaɓɓun kamfanonin Indiya ba, da suka haɗa da Reliance.

Mukesh Ambani

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mukesh Ambani zai iya samun nasara kan Amazon saboda gatan zamowarsa ɗan ƙasa

Kamfanin Future, wanda ya fi yin kasuwancin da ya shafi kayan gini, sannan annobar cutar korona ta yi masa illa, ya ce yarjejeniyarsa da kamfanin Reliance yana da muhimmanci wajen hana shi durƙushewa.

Bayyana a gaban kotu dka yi na baya-bayan nan ya shafi kamfanin Future Group ne. A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne, Babbar Kotun Delhi ta sauya matakin da ta ɗauka makon ɗaya da ya wuce wanda ya dakatar da cinikin.

Sai dai Amzaon ya ɗaukaka ƙara.

Me zai faru?

Idan har aka bar cinikin sayen Reliance ya ci gaba, zai bayar da damar sayar da kaya ɗaidai ga kantuna 1,800 a biranen Indiya fiye da 420, da kuma kasuwancin sayar da kayan sari na kamfanin Future Group.

"Reliance na da kuɗi da kuma faɗa a jin da ake buƙata a kasuwar. Ba sa buƙatar ƙwarewar yin kasuwancin intanet," in ji Mr Meena.

Idan kuma Amazon ya yi nasara, zai samu tagomashin rage tasirin shirin abokin adawarsa na kutsa wa cikin kasuwancin intanet.

Presentational grey line

Gasa

Man with shopping bags in front of Reliance grocery store.

Asalin hoton, Getty Images

Amazon da Reliance sun shirin gwabzawa ne a kan kasuwaci a Indiya saboda ganin yadda take haɓaka sosai.

"Babu wata ƙasa da take da kasuwa mai haɓaka sosai da suke samun irin wannan damar irinta Indiya, idan ka cire Amurka da China," a cewar Mista Meena.

Darajar kasuwar sayar da kaya ɗai-ɗai ta Indiya ta kai kusan dala biliyan 850, a cewar Mr Meena, amma a yanzu haka kaso kaɗan ne ke yin kasuwancin intanet.

Amma wani hasashe ya nuna cewa kasuwar ta Indiya za ta bunƙasa da kashi 25.8 cikin 100 a shekara inda zai kai dala biliyan 85 nan da shkearar 2023.

A sakamakon hakan ne kasuwancin intanet yake ƙaruwa kuma gasa ta yi yawa.

Sayen kayan masarufi ɗai-ɗai shi ne mafi girma a Indiya, saboda ƴan ƙasa na kashe rabin kuɗɗensu kan hakan.

Presentational grey line