Mai kudin duniya Jeff Bezos: Abu biyar game da attajirin da ya fi kowa kudi a duniya

Jeff Bezos
Bayanan hoto, Jeff Bezos: Attajiri mai lamba daya a fadin duniya

An kiyasta kudin Mista Bezos ya kai $200bn, bayan da ya karu cikin watannin farko na wannan shekarar yayin da annobar korona ke kara yaduwa a duniya.

Yana cikin mutanen da ke da yakinin kai dan Adam zuwa wasu duniyoyi da sararin samaniya daga doron kasa ta hanyar rokokin da yake kerawa.

Ga abubuwa biyar game da attajiri Jeff Bezos.

Jeff Bezos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Attajirin duniya na daya Jeff Bezos

Yaro mai hazaka

Tun yana dan shekara biyar, attajiri Jeff Bezos ya fara nuna hazakarsa. Cikin abubuwan ban mamaki da ya yi shi ne kwance wani gadon kananan yara da iyayensa suka sayo masa domin ya mayar da shi tamkar gado irin na manya.

Tun yana karami ya fara kwance-kwance da hade-haden na'urorin gidansu.

A misali ya hada wata kararrawa mai amfani da lantarki wadda ya rika amfani da ita domin ta sanar da shi duk lokacin da kannensa suka shiga dakinsa.

Wani abin da ya ce ba zai manta da shi ba shi ne yadda ya sanar da wata innarsa yawan shekarun da ta rage daga yawan shekaru rayuwarta saboda tana shan taba.

Wannan ya zama masa abin damuwa daga baya saboda yadda ya sanya innar tasa ta fashe da kuka.

Bezos ya ce kakansa ya ja shi gefe guda inda ya gaya masa cewa, "Wata rana za ka gane cewa ba ko yaushe ne ya dace ka nuna wayonka ba."

The relationship between Jeff Bezos and Crown Prince Mohammed bin Salman soured after Jamal Khashoggi's murder

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jeff Bezos da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman

Bezos mayen alkaluma ne

Masu neman aiki a kamfanin Amazon na fuskantar kalubale iri-iri. Tun farko Mista Bezos kan nemi masu neman aiki a kamfanin nawa suka samu a jarabawar da aka yi musu.

Bayan sun sanar da shi, sai ya koma ya kara wa jarabwar wahala domin wadanda suka fi masu neman aikin na farko ne kawai za su tsallake siratsin da ya gindaya musu.

Da ya ga masu hazaka na karuwa a kamfanin, sai ya rika sallamar duk wadanda ba su yi kokari sosai ba a jarabawar kama aiki da kamfanin.

A cikin kamfanin na Amazon, ma'aikata sun sha koka wa da yadda ake musu kiddidigan mintunan da suka dauka na zagayawa bayan gida.

Akwai kuma wasu na'urori da ke auna yawan aikin da kowane ma'aikaci ya yi a tsawon yini.

Short presentational grey line

Aiki a kamfanin Amazon sai jajirtacce

Tun kafin ya zama shahararren attaijiri, Mista Bezos ya kasance mai tafiyar da harkokinsa ta wata hanya da sauran mutane suka dauka ba daidai ba ce.

A shekara ta 1994 ya bude shagonsa na farko inda ya rika sayar da littatafai a garejin ajiye mota na gidansu.

Tun ba a je ko ina ba, Bezos ya rika sanar da wadanda suka zuba jarinsu cikin kamfanin nasa cewa cikin kashi 70 cikin 100 kamfanin na iya rugujewa kuma sun yi asarar dukkan jarin nasu kenan.

Tun wancan lokacin ya fitar da wasu tsare-tsare da yake bi wajen tafiyar da harkokin kasuwancinsa.

A misali, yafi son a rubuto masa doguwar takarda cike da bayanai a lokacin da yake ganawa da ma'aikatansa.

Yana da wata dabi'a kuma da yake kira "maitar kula da kwastomominsa". A sane yake cewa duk wanda ke da wani korafi kan wani abu da kamfanonin Bezos suka yi na iya aika masa da sakon imel kai tsaye.

"Adireshin imel dina shi ne [email protected], sananne ne, kuma ban taba boye shi ba."

Idan Bezos ya ga korafin da wani ya aiko masa, ya kan tura imel din ga wani daga cikin ma'aikatansa, inda a ciki ya kan rubuta alamar tambaya ne kawai.

Ma'anar haka ita ce ma'aikacin ya ajiye komai a gefe domin mayar da hankali kan warware matsalar da ke cikin imel din.

Wannan layi ne

Karon batta da ƴan siyasa

A shekarar 2018, Shugaba Trump na Amurka ya zargi Jeff Bezos da aikata laifuka kamar kaucewa biyan haraji da kokarin korar kishiyoyinsa ƴan kasuwa.

Sukar ta Mista Trump ta sa hannayen jarin kamfanin ya fadi da kimanin kashi 9 cikin 100, inda yawan kudinsa kuma ya ragu da kimanin dala biliyan 10, amma daga baya ya mayar da kudin.

Sanata Bernie Sanders ma ya dauki mataki kansa, inda ya jagoranci kafa wata doka a majalisar Amurka mai suna "Dokar A Dakatar da Bezos".

Sanata Sanders ya soki yadda Mista Bezos ke tafiyar da harkokinsa na kasuwanci, har yana cewa ma'aikatan Amazon na talaucewa don tsabar neman riba.

A sanadiyyar wannan sukar Mista Bezos ya kara yawan albashin da yake biyan ma'aikatansa zuwa dala 15 a kowace sa'a.

Jeff Bezos and Elon Musk

Bezos ya mayar da hankali kan tafiye-tafiye zuwa wasu duniyoyi

Bezos na zuba dala biliyan daya a kowace shekara cikin kamfaninsa na Blue Origin da ke shirin fara jigilar mutane da na'urori zuwa sararin samaniya har ma da wasu duniyoyin.

Ya ce, "Wannan ne aiki mafi muhimmanci da nake yi a rayuwata. Ina dan shekara biyar da haihuwa Neil Armstrong ya sauka adoron duniyar wata, kuma tun lokacin na kallafa a zuciyata cewa sai na binciki sararin samaniya har ma in tafi can."

Tun Bezos na makarantar sakandare ya fara tunanin yadda zai kawo sauyi ga rayuwar dan Adam a wannan duniyar da ma sauran duniyoyin da ke kusa da ta mu.

Wannan layi ne