'Yariman Saudiyya bai yi wa Jeff Bezos kutse a Whatsapp ba'

Yariman Saudiyya da Jeff Bezos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dangantaka tayi tsami tsakanin dan kasuwar da yariman Saudiyya tun bayan kisan Khashoggi

Hukumomin Saudiyya sun musanta zargin da ake yi wa yariman kasar Muhammad Bin Salman na kutsa wa wayar hamshakin dan kasuwar nan mamallakin kamfanin Amazon, wato Jeff Bezos.

Ofishin jakadancin kasar a Amurka ya bayyana zargin a matsayin mara tushe ballantana makama, tare da bukatar aiwatar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamari.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Saudiyya da biloniyan dan kasuwar wanda kuma shi ne mamallakin fitacciyar jaridar nan ta Amurka wato 'Washington Post', bayan kisan daya daga cikin marubutanta Jamal Khashoggi da ake zargin yariman da yi.

An yi kutse wayar dan kasuwar ne bayan samun wani sako ta WhatsApp dinsa a watan Mayun 2018, kuma yariman Saudiyyan Muhammad Bin Salman ne ya aika masa da sakon kamar yadda Jaridar Guardian ta ruwaito.

whatsapp

Asalin hoton, Reuters

Wani bincike da aka kaddamar dangane da laifin kutsen da ya sabawa ka'idar bayanan sirri ya nuna cewa jim kadan bayan latsa mashigin wani bidiyo da yariman ya aika masa sai kawai wayar ta fara fitar da dumbin bayanan sirrin da aka jibga mata.

Saudiyya dai ta musanta zargin.

Masu bincike a kan sahihancin bayanai sun kaddamar da bincike na musamman a kan wayar dan kasuwar a wannan watan, domin samun wasu karin bayanai.

Kamfanin Amazon ya dan yi jinkirin yi wa BBC karin bayani kamar yadda muka nema tun da farko.

An dora zargin ne kan rahoton wata cibiyar kwararru masu ba da shawara a kan harkokin tsaro da dan kasuwar ya hayo.

Ana sa ran Majalisar Dinkin Duniya za ta fitar da sanarwa a kan sahihancin zarge-zargen a Larabar nan.