Wasu 'yan Najeriya da ke rike da manyan mukamai a duniya

Nadin da aka yi wa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar kungiyar cinikayya ta duniya, WTO, a takaice, ya kara fito da martabar bakaken fata da ma kasarsa Najeriya.

Ita ce mace ta farko kuma 'yar Afirka da aka nada a kan wannan mukami.

Hakan ya sa mun yi waiwaye kan wasu daga cikin 'yan Najeriya da suka rike manyan mukamai a hukumomin duniya.

1. Dr. Ngozi Okonjo-Iweala

Okonjo-Iweala, mai shekara 66, za ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar.

Duk da cewa kwanan nan ta samu karɓi takardar zama ƴar ƙasar Amurka, tana alfahari da kasancewarta ƴar Najeriya kuma tana da kishin ƙasa - tana nuna asalinta na Afirka ta hanyar tufafin da suka dace da Afirka.

Ta taɓa faɗa wa BBC a 2012 cewa ta rungumi irin tufafinta a matsayin uwar yaƴa huɗu ma'aikaciya, ta ƙiyasta tufafin da take saka wa na atamfa kowanne ya kai kimanin dala $ 25.

Masaniyar tattalin arzikin da ta ya yi karatu a Jami'ar Harvard a matsayin mai kwazo da jajircewa, kamar yadda ta faɗa wa BBC HardTalk a watan Yuli cewa abin da WTO ke bukata shi wanda zai tabbatar da sauyi.

A cikin shekaru 25 da ta yi a Bankin Duniya, an yaba mata ga wasu tsare-tsare don taimakawa kasashe masu karamin ƙarfi, musamman tara kusan dala biliyan 50 a shekarar 2010 daga masu ba da tallafi ga Kungiyar Ci Gaban Kasa da Kasa (IDA), gidauniyar Bankin Duniya ga kasashe matalauta.

Amma sauyin da ta kawo a Najeriya shi ne take alfahari da shi - musamman kasancewar sau biyu da ta riƙe matsayin ministar kudin ƙasar a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

2. Dr Mohammed Sanusi Barkindo

An haifi Mohammed Sanusi Barkindo a ranar 20 ga watan Aprilun shekarar 1959 a jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya.

Barkindo gogaggen dan boko ne kuma kwararre a fannin albarkatun man fetur.

A ranar daya ga watan Augusta ne Barkindo - wanda tsohon shugaban babban kamfanin mai na Najeriya NNPC ne - ya fara aiki a matsayin Sakatare Janar na kungiyar kasashe masu fitar da danyen man fetur OPEC.

Ya taba rike mukamin shugaban rikon kwarya na kujerar sakatare janar din na kungiyar ta OPEC a shekarar 2006.

Kuma a cikin shekarar ne gwamnatin Najeriya ta tsayar da shi a matsayin wanda zai nemi mukamin.

A taron kungiyar ta OPEC na 169 a ranar 2 ga watan Yunin shekarar 2016 ne a sakatariyar kungiyar da ke birnin Vienna na kasar Austria aka sanar da mukamin na Barkindo a matsayin sabon sakatare janar na OPEC.

Ya kuma karbi ragamar jagorancin ne daga hannun ministan mai na kasar Libya Abdalla El-Badri, wanda wa'adin mulkinsa yake kare.

Karatunsa

Dr Mohammed Sanusi Barkindo ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria a Nigeria, inda ya samu takardar shaidar kammala digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa, ya kuma yi karatun babbar difiloma a fannin tattalin arzikin man fetur a Kwalejin Nazarin Albarkatun man fetur a Jami'ar Southeastern ta Amurka.

Mr Barkindo ya kuma karo karatu a fannin tattalin albarkatun man fetur daga Kwalejin albarkarun man fetur ta Jami'ar Oxford, da kuma digiri na biyu a harkokin kasuwanci daga Jami'ar Southeastern da ke birnin Washington, DC a Amurka.

Yana kuma da takardar shaidar kammala karatun digirin digirgir a fannin kimiyya daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Modibbo Adama, da ke jihar Adamawa a Najeriya.

Ayyuka da mukamansa

Barkindo ya rike mukamin shugaban babban kamfanin mai na Najeriya NNPC daga shekarar 2009 zuwa 2010.

Kafin nan, ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin manajan daraktan hukuma tace iskar gas ta Najeriya da hadin gwiwar kamfanonin mai na NNPC, da Shell, da Total da kuma Eni.

Ya kuma taba rike mukamin mataimaki na musamman ga tsohon ministan mai na Najeriya kuma tsohon Sakatare Janar na kungiyar ta OPEC Dr Rilwanu Lukman.

Barkindo ya kuma yi aiki a muhimman bangarori a kungiyar ta OPEC daga shekarar 1986 zuwa 2010.

Kwararre a fannin albarkatun man fetur da iskar gas da kuma harkokin kungiyar ta OPEC, Barkindo ya yi amfani da gogewar da yake da ita a ciki da wajen Najeriya wajen tafiyar da jagorancin.

3. Amina J. Mohammed

Amina J. Mohammed 'yar siyasa ce kuma jami'ar huddar diflomasiyya a Najeriya wacce yanzu haka take rike da mukamin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

An haife ta a ranar 27 ga watan Yunin shekarar 1961 a jihar Kaduna, kuma mahaifiyarta Baturiya ce, wacce mahaifinta dan Najeriya ya auro a kasar Birtaniya lokacin da ya je can karatu. Kuma ita ce babba a cikin 'yaya mata biyar da suka haifa.

Karatunta

Malama Amina Mohammed ta kammala karatunta na firamare a makarantar Kaduna Capital a shekarar 1972. Daga nan ne ta tafi kasar Birtaniya inda ta yi karatun sakandare a makarantar Buchan School Isle ta birnin Manchester a shekarar 1989.

Amina ta samu takardun shaidar karatun digirin girmamawa da dama kuma ta yi aikin koyarwa a fannin raya kasashen duniya a Jami'ar Columbia ta Amurka.

Ayyuka da mukamanta

Yanzu haka Hajiya Amina Mohammed na rike da mukamin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

Amina ta kuma rike manyan mukamai da dama da suka hada da mai taimaka wa shugaban Najeriya ta musamman kan shirin muradun Majalisar Dinkin Duniya na (MDGs).

In 1981, malama Amina ta fara aiki da kamfanin Archcon a Najeriya, kamfanin da ke gudanar da ayyukan zayyana gine-gine da hadin gwiwar kamfanin Norman and Dawbarn na kasar Birtaniya.

A shekarar 1991 ta bar aiki a kamfanin inda ta kafa kamfanin kwangilar gine-gine na Afri-Projects Consortium, inda ta rike mukamin babbar darakta a shekarar 2001.

A tsakanin shekarar 2002 zuwa 2005, Amina Mohammed ta jagoranci kwamiti kan ilmi da kuma jinsi a karashin shirin Muradin karni na Majalisar Dinkin Duniya.

Daga bisani ne ta samu mukamin babbar mai taimaka wa shugaban Najeriya na shirin Majalisar Dinkin Duniya na (MDGs).

A shekarar 2015, Amina Mohammed ta samu mukamin Ministar Muhalli, wanda ta rike har ya zuwa watan Fabrairun shekarar 2017.

A cikin watan Janairun shekarar 2017 ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya sanar da ba ta mukami a matsayin mataimakiyarsa.

4. Akinwumi Adeshina

Akinwumi Adesina tsohon Ministan Ayyukan gona da raya karkara ne a Najeriya, kuma yanzu haka yana rike da mukamin shugaban babban bankin raya kasashen Afirka ADB.

Dakta Akinwumi Adeshina, daya daga cikin mashahuran 'yan bokon Najeriya ne da suka yi fice a fannin samun manyan mukamai na kasashen duniya, bayan da ya zama dan Afirka na farko da ya samu mukamin shugaban babban bankin raya kasashen Afirka ADB a shekarar 2015.

An haifi Dr. Akinwumi Akin Adesina a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 1960 a birnin Ibadan na jihar Oyo kudu maso yammacin Najeriya.

Ya fara karatun firamare da na sakandare a makarantun da ke garinsu, kafin daga ya ci gaba zuwa Jami'ar Ife a Najeriya inda ya kammala da digirin farko a fannin ayyukan noma da tattalin arziki da sakamako mafi girma.

A shekarar 1984 ne Akinwumi ya kuma kammala karatunsa a Jami'ar Purdue da ke jihar Indiana ta Amurka, inda ya halarta don karo karatu, ya kuma dawo gida Najeriya lokacin da ya auri matarsa Grace.

Dakta Akinwumi ya kuma takardar kammala karatun digirin digirgir a fannin ayyukan noma da tattalin arziki a shekarar 1988, inda ya kuma yi fice da samun lambar yabo kan nazarin ayyukan binciken nashi.

Ayyuka da mukamansa

Dakta Akinwumi Adeshina ya fara samun mukamin zama babban masanin tattalin arziki a kungiyar bunkasa noman shinkafa ta Afirka ta yamma (WARDA) a birnin Bouaké na kasar Ivory Coast daga shekarar 1990 zuwa 1995.

A shekarar 2010 ne Adesina ya samu mukamin Ministan Ayyukan Gona na Najeriya, mukamin da ya rike har ya zuwa shekarar 2015.

Wasu daga cikin kyawawan ayyukansa sun hada da bullo da shirin yadda za a raba taki ga manoma a bisa tsari mafi kyau.

Ya kuma fito da tsarin bai wa manoma wayoyin salula, don saukaka musu wajen samar da takin zamanin, duk da cewa shirin ya gamu da cikasa saboda rashin hanyoyin sadarwa a akasarin yankunan karkara a Najeriyar.

Akinwumi Adesina ya kasance dan Najeriya na farko da ya samu babban mukamin shugaban bankin raya kasashen Afirma ADB, bayan da ya samu galaba a zaben da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2015.

A lokacin da yake rike da mukamin Ministan Gona a Najeriyar ne a shekarar 2010 Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nada shi a matsayin daya daga cikin shugabannin duniya 17 da suka jagoranci shirin nan na burin raya kasashe na majalisar dinkin duniya na MDG.

Ya kuma yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kungiyar hadin gwiwa kan hadakar aiwatar da manufofin bunkasa ayyukan gona a Afirka (AGRA).