Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jelani Aliyu: Bahaushen da ya zana fitattun motocin da ake hawa a duniya
Latsa wannan hoto na sama domin sauraron Jelani Aliyu
Jelani Aliyu, dan asalin jihar Sokoto da ke Najeriya, ya yi aiki da kamfanin kera motoci na GM Motors da ke Amurka kuma shi ne mutumin da ya zana mota kirar Chevrolet Volt da sauran nau'in motoci.
Jelani ya shaida wa BBC cewa: "Bayan na kammala karatuna a Amurka, ina shirin komawa gida Najeriya sai kawai wani abokina ya ce kamfanin GM Motors ya kira yana son ya ba ni aiki. Hakan ya sa na kira su kuma suka tabbatar min."
A shekarar 2017 ne shugaba Muhammadu Buhari ya neme shi da ya koma Najeriya domin samar da gyara ga hukumar zayyana motoci da tsara su ta Najeriya wato NADDC.
Burin Jelani Aliyu shi ne samar da matasa 'yan Najeriya kamarsa sannan ya tabbatar da an samar da motoci masu amfani da wutar lantarki a Najeriya.