Ku San Malamanku tare da Sheik Hassan Abubakar Dikko
Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheik Hassan Abubakar Dikko a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon:
Sheik Hassan Abubakar Dikko, fitaccen malami na kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a wa ikamatus-sunna, ya ce ba zai iya bai wa wanda ba akidarmu daya ba auren 'yarsa.
A hirarsa da BBCa cikin filinmu na Ku San Malamanku, malamin ya bayyana tarihin rayuwarsa da irin gwagwarmayarsa ta karatun addini da rayuwa.
Ya ce shi cikakken dan kungiyar da aka fi sani da Izala ce assasawar Sheik Ibrahim Zakariyya wacce take a garin Jos, karkashin Sheik Sani Yahaya Jingir.
Yana rike da mukamin shugaban majalisar malamai na jihar Filato na kungiyar.
Wane ne Sheik Hassan Abubakar Dikko?
An haifi Sheik Hassan Abubakar Dikko a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma ya taso ne a gaban kakansa wani shahararren malamin addinin Musulunci Idris Zakariyya, wanda shi ya tarbiyantar da shi.
Ya bayyana cewa daga nan sai kawunsa mai suna Isma'ila Idris ya dauke shi zuwa garin Kaduna inda ya ci gaba da zama a gabansa har lokacin da Allah ya kaddari ya bar aiki daga kungiyar Jama'atul Nasril Islam ya shiga aikin soja.
Malamin ya ce daga nan ne ya samu hanyar da zai ci gaba da rayuwa da gwagwarmayar neman karatu a gaban malamai.
"Na zauna a gaban Sheik Abubakar Mahmud Gumi na yi karatu gwargwadon hali, daga nan na samu damar zuwa makarantar koyon harshen Larabci ta Kano (SAS)," in ji shi.
Ya kuma ce bayan kammala karatun nasa a makarantar ta (SAS) Kano, ya sake dawowa garin Kaduna inda ya kama aikin gwamnati na koyarwa a makarantar firamare har ya kai matsayin shugaban makaranta (hedimaster).
Sheik Dikko ya kara da cewa a wannan lokacin ne kawun nasa wanda ya shiga aikin soja wato Sheik Isma'ila Idris ya koma birnin Jos ya bar aikin soja, inda ya kafa kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a wa Ikamatus Sunna.
"Wa'azi ya kankama sai ya bude makarantar ilmin addinin Islama mai zurfi, daga nan ya nemi in dawo garin Jos na zauna tare da shi domin ci gaba da karantarwa a makarantar. Dawowa Jos ta ba ni damar ina koyarwa na shiga jami'a, na yi digirina na farko, amma digirina na biyu na yi shi ne a fannin addinin Musulunci da harshen Larabci," in ji malamin.
Sheik Hassan Dikko ya ci gaba da aikin koyarwa, inda daga bisani ya shiga aikin gwamnati a siyasance a jihar Bauchi zamanin mulkin Ahmed Adamu Mu'azu.
A cewarsa: "Bayan mun kammala shekara takwas da shi na yi shekara biyu da Malam Isa Yuguda wanda ya gaje shi, sai na sake komawa jami'a don nazarin digiri na uku a Jami'ar jihar Nassarawa a cikin garin Keffi."
Gwagwarmayar kungiyar Izala
Malamin ya kuma bayyana wa BBC irin kalubale da kuma gwagwarmayar da suka sha a makaranta shi da wasu daga cikin daliban da ke da akidar Izala, ganin cewa ba ta samu karbuwa a garin Kano ba.
Ya ce: "An yi gwagawrmaya wacce ta ke ba karama ba. Lokacin da aka kafa ta ina makaranta a Kano kuma ina tare da akidarta, amma da yake lokacin ga yadda Kano take, boye akidarmu muke yi, ba ma iya bayyana ga inda muke, don haka idan ana magana a aji sai mu yi gum da bakinmu amma kuma duk da haka bai hana a gano mu ba."
Sheik Dikko ya ce: "Allah da ikonsa daga baya wadanda suka zamanto suke fada da Izala su ne aka wayi gari su ne shuwagabanni, su ne jagorori, malaman da suke sukan Izalar aka wayi gari suke wa'azi."

Ba zan iya bai wa wanda ba mai irin akidata 'yata ya aura ba
Sheik Hassan Abubakar Dikko ya shaida wa BBC cewa ba zai iya bayar da auren 'yarsa ga wanda ba akidarsu ta addini daya ba a bisa wasu dalilai da ya bayyana.
"Idan wani wanda yake da akidata da ta shi ba daya ba, ya zo yana neman auren 'yata ba zan iya ba shi ba, saboda ban amince da shi ba, saboda haka ba zan dauki jinina in ba shi ba, don ban san me za su haifa ba," in ji malamin.
Da yake an ce rai dangin goro ne, malamin ya karkare hirar tasa da BBC yana mai cewa a lokacin da ba ya karatu ba ya wani aiki, babban abin da yake yi ya sanya shi nishadi shi ne ya zauna ya rika tuna wuraren da suka je suka yi da'awa, da adadin mutanen da suka musulunta ko kuma mutanen da suka fahimci gaskiya.
"Idan ba na karatu ba na aiki ba na komai sai kwakwalwata ta rika tuno min da mutanen alkhairi wadanda fahimtarmu ta zo daya, idan ba na karatu ba na aiki sai in rika tuna mutanen da Allah ya ciyar da su gaba ta fuskar ilimi ko ta fuskar dukiya amma a halin yanzu suna taimakon addini, in ji shi.
Kana ya ce babban burinsa shi ne ya cika da kalmar shahada.












