Rikicin yankin Tigray : Yadda ƴan gudun hijirar yankin ke yin kalaci da ganyen bishiya don su rayu

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyun ɓangaren adawa a yankin Tigray na kasar Habasha, sun ja hankalin duniya su na cewa: da akwai babbar barazana ga rayuwar jama'a idan ba a kai taimakon gaggawa ba.
Tuni dai mutane ke ta mutuwa sanadiyar rashin abinci, shi ya sa a cewar jam'iyyun su ke kira ga kasashen duniya su kai musu agaji.
Gwamnatin Habasha na cewa ana kai kayan agaji, kuma tuni suka shiga hannuwan mutanan da yawan su ya kai milyan daya da rabi.
Jam'iyyun sun sanar da cewa mutane dubu 52 ne aka kashe tun lokacin da ricikin ya ɓarke a cikin watan Nuwanba zuwa yanzu.
To sai dai kuma ba su yi wani ƙarin bayani ba kan yadda suka yi ƙididigar yawan mutanan da suka mutun, amma sun sanar da cewa daga cikin wadanda suka mutun, sun hada da mata da yara da shugabanan addini .
Daga ɓangaren gwamnatin kasar babu wasu al'kalumma da ta bayar, sai dai ta na cewa ta na kokarin daukar matakin doka kan tsohuwar jam'iyyar dake mulki a Tigray.
Tashin hankali ya ɓarke ne bayan da jam'iyyar TPLF ta Tigray People's Liberation Front ta mamaye barikin sojojin ƙasar a yankin, abun da ya haddasa tabarbarewa dangantaka da gwamnatin Firai minista Abiy Ahmed.
Yadda yaƙin ya raba mutane da matsugunansu

Asalin hoton, SOCIAL MEDIA
Kimamin 'yan gudun hijira daga kasar Eritriya dubu dari da ke rayuwa a cikin sansanonin 'yan gudun hijira na majalasar dinkin duniya a Tigray kuma lamarin rikicin ya rutsa da su.
Kakakin hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalasar dinkin duniya ya sanar da cewa yawancin 'yan gudun hijira da lamarin ya rutsa da su, na cin ganyayen bishiyoyi ne da kuma shan ruwan sama da suka kwanta a cikin tabkuna bayan da aka tilasta masu ficewa daga sansanonin.
Rikicin na Tigray ya kuma raba aƙalla mazauna yankin miliyan biyu daga matsugunansu saboda gudun tashin hankali.
A ranar Litanin,babban jami'in hukumar 'yan gudun hijira ta kasar Norway ,Jan Egeland ya sanar da cewa ,a cikin sama da shekaru 40 da ya ke aikin jinkai, bai taba ganin yadda lamarin agaji su ka yi rauni ba a filin aiki kamar wannan karo.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa. jam'iyun bangaren adawa guda uku da suka haɗar da Tigray Independence Party (TIP) da Salsay Weyane Tigray da kuma National Congress of Great Tigray, sun sanar da cewa abinci da magungunna ba su zuwa da wuri, kuma wannan abun ya sa tabarbarewar lamura da kuma birkicewar rayuwa a yankin.
An nakasa birane da kauyukan yankin ta hanyar sakin boma-bomai da ake harbawa.
An kwashe tare da wargazar da kayayakin kiwon lafiya da na bayar da illimi, kuma wani babban abin mamaki a cewar jam'iyyun adawar ,shi ne hatta da wuraren su inda suke gudanar da ibadodinsu an kai masu hari an ruguza su.
Wani hoto ya nuna wasu mutane dubu 60 daga yankin Tigray na rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar Sudan.
Ƙasashen duniya sun caccaki hukumomin Habasha

A makon da ya gabata kasar Amurika ta yi kira da a janye dakarun kasar Eritreya ba tare da wani jinkira ba, ta kuma kara da cewa rahotanni marasa dadi na fitowa daga yankin wadanda suke nuna cewa an keta hakin bil adama ta hanyar gudanar da fyde da kuma kwasar ganimati.
To sai dai tuni gwamnatin kasar Habasha da ta Eritereya suka musunta cewa babu dakarun kasar Eritereya a yankin Tigray.
Jam'iyyar TPLF ta jagoranci yankin Tigray da kusan baradan yaki dubu dari biyu da hamsin a karkashin ikonta na kusan shekaru 30..
Jam'iyar ta sauka daga kan mulki ne bayan da dakarun gwamnatin Habasha suka karɓi mulki da babban birnin Mekelle a ranar 28 ga watan Nuwanba.
Firai ministan Habasha Mista Abiy Ahmed, na zargin jam'iyyar ta TPLF da yin barazana ga mutuncin da yancin kasar Habasha, ta hanyar kokarin kifar da gwamnatin shi bayan jam'iyyar ta karbe tare da mamayar wani barikin sojoji na tsawon wata daya .
A cikin watan Agusta an gudanar da zaɓen a yankin na Tigray wanda ya kasance zakaran gwajin dafi kan matakin da ya dace a dauka daga gwamnati,
Gwamnatin Mista Abiy ta ayyana zaben a matsayin haramtace, a yayin da ita kuma jam'iyyar ta TPLF ke cewa gwamnatin Habasha haramtacciya ce kuma ba ta da wani hurumi na ta mulki Tigray.
Ga ƙarin wasu labaran masu alaƙa da wannan.











