Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ƙidayar giwaye daga sararin samaniya
- Marubuci, Daga Victoria Gill
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent, BBC News
Hoto na farko da aka ɗauka da tauraron ɗan Adam, ya nuna wasu abubuwa kamar ƙwallo mai launin toka a tsakiyar korayen bishiyun - amma idan aka yi kallon tsanaki, za a gane waɗannan abubuwan masu kamar ƙwallon giwaye ne ke ta watangaririya a tsakanin bishiyu.
Masana kimiyya kuma na amfani da waɗannan hotuna suna ƙirga yawan giwayen da ke Afrika.
An samu hotunan ne daga wani tauraron ɗan Adam mai nisan kilomita 600 daga doron ƙasa.
Wannan tauraron ɗan Adam na iya ba da damar ganin kilomita 5,000 na inda giwaye ke rayuwa a duk ranar da babu hadari.
Kuma ana gudanar da aikin ƙidayar giwayen mai matuƙar wahala ne da wata komfuta da aka horar don gano giwaye a wurare daban-daban.
"Muna gabatar da wannan misalin ne … kuma mu bayyana shi, wannan giwa ce, wannan ba giwa ba ce, in ji Dakta Ogla Isupova, na Jami'ar Bath.
"Ta hanyar yin hakan, za mu iya yiwa injinanmu setin da za su iya ba da bayanai kan ƙaramin abu, wanda ba za a iya gani da idanu ba."
Da farko masana kimiyyar sun duba gidan namun daji na Addo da ke Afrika ta Kudu.
"Yana da yawan giwaye, "In ji Dakta Isla Dupoge na Jami'ar Oxford.
"Kuma yana da yankunan da suke da bishiyoyi masu duhu sannan kuma ga fili.
"Don haka wuri ne mai kyau da za mu iya gwada abin da muka zo da shi.
"Wannan wani sabon ilimi ne da ya ke daf da bayyana.
"Kuma manyan ƙungiyoyin masu fafutukar kare muhalli sun nuna sha'awarsu kan amfani da shi domin maye gurbin amfani da jiragen sama."
Masu fafutukar kare muhalli za su riƙa biyan kuɗi don amfani da taurarin ɗan Adam ɗin da hotunan da suke ɗauka.
Amma wannan tsarin zai taimaka wajen yadda za a riƙa bin giwayen da ake fargabar rayuwarsu na fuskantar barazana a wuraren da suka ratsa iyakoki, inda da wahala a samu damar yin bincike da jiragen sama.
Masana kimiyya sun ce za a iya amfani da wannan tsarin wajen yaƙi da masu farauta ba bisa ƙa'ida ba.
"Kuma tunda za ka iya ɗaukar hoton daga sama, ba ka buƙatar kowa a ƙasa. Wannan zai iya taimakawa a wannan lokaci na annobar Korona," in ji Dr Duporge.
"A ɓangaren binciken rayuwar dabbobi, ba a fiye samun ci gaba a fannin fasaha ba.
"Don haka samun damar amfani da sabbin hanyoyin fasaha wajen kare haƙƙin dabbobi abu ne mai kyau."