Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Singapore: Za a fara ƙirƙirar naman kaza a ɗakin binciken kimiyya
Singapore ta zama ƙasa ta farko da ta amince a riƙa sayar da naman da ake haɗa wa a daƙin gwajin kimiyya.
Matakin ya buɗe kofa ga kamfanin Amurka na Eat Just ya riƙa sayar da naman kajin da yake haɗawa a cikin daƙin gwaji.
Ana samar da naman ne ta hanyar ƙwayoyin halittun dabobbi sannan a sarrafa su ta yadda za su sake girma a daƙin gwaji.
Mamallakin kamfanin mai suna Josh Tetrick ya ce naman da ɗaƙin gwajin ke samarwa ta wannan hanya ya fi lafiya da kuma dacewa da muhalli sama da wanda aka saba gani na ƙyanƙyasar ƙwai.
Wakiliyar BBC ta ce babu mamaki wannan ya ja hankalin sauran kamfanonin da ke gogayya a ƙasashen duniya na aminta da wannan tsarin samar da naman.
A cewar Bankin Barclays, kasuwar da wannan harka za ta yi za ta kai darajar dala biliyan 140 cikin shekara 10 masu zuwa, ko kusan kashi 10 cikin 100 na jumullar kuɗin da ake juyawa a masana'antar samar da naman kaji na dala tiriliyan 1.4.
Gagarumar nasara
Kamfanin ya kira lamarin da gagarumar nasarar da ba a taɓa samun irinta ba a masana'antar samar da abinci ta duniya, tare da fatan sauran ƙasashe za su bi sahu.
A cikin shekara 10 da suka gabata, gwamman kamfanoni sun yi ƙoƙarin gabatar da naman a kasuwa, da fatan za su yi nasarar saye zuciyar masu son cin naman tare da alƙawarin samar da ingantacce mai lafiya.
Biyu daga cikin manyan kamfanonin duk a Isra'ila suke, Future Meat Technologies da kuma the Bill Gates-backed Memphis Meats, waɗanda dukkansu ke ƙoƙarin shiga kasuwar ta hanyat samar da ingantaccen nama mai ɗanɗano da ake samarwa a ɗakin gwaji.
A yayin da wasu ke cewa samar da naman a ɗakin gwaji zai taimaka wajen inganta muhalli, wasu masana kimiyya na ganin hakan ƙara lalata muhalli zai yi.
Sannan masu sharhi na cewa irin wannan nama da ake samar wa a ɗakunan gwaji sun fi tsada sosai fiye da wanda ake kiwata.