Rotimi Akeredolu: Gwamnan Ondo ya bai wa makiyaya kwana bakwai su bar dazukan jihar

Lokacin karatu: Minti 2

Fulani makiyaya a jihar Ondo sun ce sanarwar da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya yi na cewa ya ba su kwanaki bakwai su bar dazukan jihar ya zo masu da mamaki.

Sarkin Fulani na jihar Alhaji Ali Dogo ya ce sanarwar ta zo masu da mamaki ne saboda sun cimma matsaya da gwamnan jihar a baya.

"Ban ji daɗi ba saboda mu ƙungiyar Fulani makiyaya mun je har gaban gwamna, aka ce mu haɗa kai da gwamnan zai ba mu kayan aiki mu yi maganin duk wani mugu.

"Idan bafulatani ya yi ɓarna mun yarda a kama shi dole ya biya ɓarnar da ya yi. Amma bafulatani na daji da shanun shi sai a ce ya yi garkuwa da mutane, ya yi sata. Duka wannan ba gaskiya ba ne," a cewar Alhaji Ali Dogo.

Gwamna Akeredolu ya bai wa makiyaya wannan wa'adi ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin inda ya ce su ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.

"A yau mun dauki manyan matakai na warware matsalolin satar mutane a hannu daya, da kuma sauran miyagun laifuka wadanda rahotanni kan tsaro da 'yan jarida da kuma wadanda lamarin ya rutsa da su a jihar Ondo suka yi ciakken bayani a kansu," in ji gwamnan.

A cewarsa: "Galibin wadannan matsaloli ana danganta su da wasu bara-gurbi da ke fakewa da sunan makiyaya . Wadannan masu aikata laifuka sun mayar da dazukanmu a matsayin wuraren da suke boye mutanen da aka sace, inda suke tattaunawa domin karbar kudin fansa sannan su aikata wasu laifukan."

Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa nan babban mai kula da sha'anin tsaro na jiharsa, ba zai zue ido ba ya bari ana ci gaba da aikata irin wadannan laifuka.

"Don haka daga yau Litinin 18 ga watan Janairu, 2021 na bayar da umarnin ga makiyaya su fice daga dukkan dazukan jihar nan nan da kwana bakwai. Haka kuma an haramta yin kiwo da daddare nan take saboda da daddare aka fi lalata gonaki," in ji shi.

A cewarsa, sun dauki matakin ne da zummar tabbatar da tsaron rayuka da na kaddarori a jihar ta Ondo yana mai bayar da umarni ga jami'an tsaro su tabbatar da an aiwatar da dukkan umarnin da ya bayar.

Gargadin da gwamnan jihar Ondo ya bayar ya zo a daidai lokacin da gwamnatin jihar Oyo ita ma ta umarci Fulani makiyaya da ke dazukanta da su bar wadannan yankuna, bisa zargin da ake yi mu su cewa ana samun baragurbi daga cikinsu da ke garkuwa da mutane.

Wannan lamari na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin makiyaya da wasu al'umomi da ke kudancin Najeriya saboda zargin da ake yi wa makiyayan da sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa.

Sai dai makiyayan sun sha musanta wannan zargi suna masu cewa wasu gwamnatocin kudancin Najeirya suna yi musu kora-da-hali.

Ko da a makon jiya sai da kungiyar Fulani makiyaya ta Gan-Allah ta zargi jami'an tsaro na kungiyar sintiri ta Amotekun da kashe makiyaya hudu a farmakin da ta kai musu.