Fulani: Ana siyasantar da lamarinmu a Najeriya'

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal-Hore a Najeriya ta koka da yadda ake "siyasantar da duk wani lamari da ya shafi Fulani a kasar".

Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah na kasa, Alhaji Bello Bodejo, wanda ya bayyana haka, ya kuma ce matukar ba a cire siyasa cikin kokarin da ake yi na shirin samar da ruga ko wuraren kiwo ga makiyaya ba, to kuwa zai yi matukar wahala gwamnatin tarayya ta samu ikon aiwatar da shirin.

Ya ce gwamnatin kasar ta bullo da shirin ne domin kawar da matsalar fada tsakanin manoma da makiyaya da kuma inganta harkar kiwo amma siyasa na kawo tarnaki ga shirin.

Gwamnatin dai a yanzu haka ta ce tana yi wa shirin samar da rugage garanbawul da kuma magance koke-koken da aka samu bayan da ta fara aiwatar da shirin a kwanakin nan.

Dama dai tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na tsugunar da makiyaya ta hanyar gina masu "ruga," 'yan kasar na ciki da wajenta suka fara bayyana mabambantan ra'ayoyi.

Gwamnatin jihohi ma ba a bar su a baya ba, inda tuni gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya suka kekashe kasa cewa ba za su shiga wannan shiri ba.

Toh sai dai a na shi bangaren Alhaji Bello, ya bayyana cewa matsalolin Fulani a Najeriya sun banbanta, domin kuwa matsalar da Bafulatanin Jos ke fama da ita ta sha bam-ban da ta Bafulatanin Enugu wanda yakamata gwamnatin ta gano bakin zaren.

Ya kuma ce idan gwamnonin arewacin Najeriya suna da iko da kasashen da suke mulki, idan sun tashi aiwatar da wani shiri da ya shafi Fulani, su aiwatar da shi kawai, wanda hakan zai jawo na kudu su ma su aiwatar.

Alhaji Bello ya ce, harda sakamakon cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Bafulatani ne ake kara siyasantar da lamarin Fulani a a kasar.