An dakatar da hukuncin hana Tripper buga wasa mako 10

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da hukuncin hana Kieran Trippier buga wasa mako 10, bayan da aka samu dan kwallon da laifin karya ka'idar yin caca.An dauki wannan matakin ne don sauraren daukaka kara da Atletico Madrid ta shigar kan dan kwallon tawagar Ingila.Wani kwamiti ne ya samu dan wasan Atletico Madrid da laifin karya ka'idar caca har guda hudu a cikin watan Disamaba.Daga nan ne aka yanke hukuncin hana shi buga tamaula mako 10 da biyan tara fam 70,000, amma yanzu an dakatar da hukuncin.
Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta ce dakatar da hukuncin ya biyo bayan da Atletico ta daukaka kara, kuma ya kamata a saurareta.Dan kwallon Ingila ya aikata laifin ne cikin Yulin 2019 a lokacin da Trippier ya koma Atletico da taka leda kenan daga Tottenham.Trippier bai buga gasar La Liga da Atletico ta doke Getafe 1-0 ranar Laraba ba.







