Erling Haaland ya taka rawar gani a 2020, ko zai ɗora a sabuwar shekara?

Asalin hoton, Getty Images
Kafin a buɗe kasuwar saye da sayar da ƴan wasan tamaula a nahiyar Turai a Janairun 2019, Erling Haaland ya koma Borussia Dortmund daga Red Bull Salzburg, wanda ya saka hannu kan kwantiragin shekara biyar.
Kafin Janairun 2020, Haaland ya ci kwallo 33 a wasa 32 tun komawarsa buga gasar Bundesliga - wannan kwazon da ya saka na nuna cewar dan kwallon Norway zai zama daya daga fitattun 'yan wasan tamaula a duniya.
Ko wacce rana Haaland ya taka a 2020 ?
1- Haaland shi ne dan wasan Dortmund na farko da ya ci zura kwallo a raga a karawar farko da ya yiwa a Bundesliga da kofin DFB da DFL Super Cup da kuma Champions League.
3 - Ya kafa tarihin cin kwallo uku rigis a wasa a 2020, wanda ya shiga wasan daga baya, sakamakon zaman benci da ya yi amma ya ci Augsburg kwallo uku - dan kwallon da ya yi haka a tarihin gasar Bundesliga.
4- Shi ne matashin da ya ci kwallo hudu a wasa a gasar Bundesliga karawar mako na takwas a fafatawa da Hertha Berling. Yana da shekara 20 da kwana 123,
5- Haaland ya ci kwallo biyar a wasa biyu a Bundesliga, ba wanda ya yi wannan bajintar.
7- Ya kuma ci kwallo bakwai, bayan buga wasan li kuku a Jamus, ba wanda ya kafa wannan tarihin a Bundesliga,
9- Haaland na saka riga mai lamba 9 a Dortmund, wadanda suka sa rigar a baya a kungiyar sun hada da Paco Alcacer da Michy Batshuayi da kuma Pierre-Emerick Aubameyang, wadanda kowanne ya ci kwallo a wasan farko da ya fara buga wa kungiyar.
19- Dan wasan tawagar Norway yana da shekara 19 da kwana 182 ya fara cin kwallo uku rigis a raga, shi ne na biyu matashin da ya yi wannan bajintar a Bundesliga. A shekarar 1965 Walter Bechtold ya zama mai karancin shekaru da ya ci kwallo uku rigis a wasa a Bundesiga.
23- Dan wasan ya ci kwallo 23 a wasa 23 a Bundesliga. Wanda ke rike da tarihin a baya a 1963-64 shi ne Uwe Seeler da ya zura 20 a raga a wasa 23.
Ranar Lahadi 14 ga watan Janairu Dortmund ke karawa da Wolfsburg a wasan mako na 14 a gasar Bundesliga, ko Haaland zai dora daga inda ya tsaya?











