Mai juna biyu ƴar shekara 13 da ke zuwa makaranta

Asalin hoton, Waves
- Marubuci, Daga Penny Spiller
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
A watan da ya gabata ne aka kai gwamnatin Tanzania kara kan haramta wa dalibai 'yan matan da ke da juna biyu da masu shayarwa zuwa makaranta.
Tana daga cikin kasashe kadan a duniya da suke tsaurara wannan haramci.
A shekarar da ta gabata ne, a kuma irin wannan watan, wata kotu ta umarci kasar Saliyo ta dakatar da wannan haramci. Don haka ta yaya abubuwa suka sauya a wannan kasa da ke yankin Afrika ta Yamma?
Shekarun Fatu (ba sunanta na gaskiya ba) goma sha uku (13), kuma tana dauke da juna biyu na wata hudu. An yi mata fyade ne. A cikin wannan shekarar, halin da ta ke ciki dai yana nufin barin ta makaranta, sannan zai iya kasancewa tabbas a yi mata auren dole.
A maimakon haka ta tsaya a kan burin da take da shi na ta ga cewa wata rana ta zama ma'akaciyar jinya.
A cikin watan Maris, kasar Saliyo ta janye haramci kan kan 'yan matan ta suka samu juna biyu ko suke shayarwa yayin da suke zuwa makaranta, watanni uku bayan da kotun Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma (ECOWAS) - ta yanke hukuncin cewa hakan ''nuna banbanci ne'' kuma ya saba wa 'yancin kananan yara kan samun ilimi.
Kasar ta dade tana fama da matsalar daukar ciki a tsakanin kananan yara - fiye da kashi 35 bisa dari na 'yan mata masu kasa da shekara 18 sun haihu a cikin shekara ta 2013. Adadin ya karu - zuwa kashi 65 bisa 100 a wasu yankunan - lokacin barkewar annobar cutar Ebola a shekarar 2014 zuwa 2015 lokacin da aka tilasta rufe makarantu.
Matakin gwamnati, bayan da kasar ta Saliyo ta farfado daga matsalar annobar Ebola, shi ne ta ayyana a hukumance haramta wa 'yan matan da ke dauke da juna biyu zuwa makaranta, don fargabar cewa za su iya ''saka sauran 'yan matan su aikata irin abin da suka aikata''.
Yayin da kididdigar hukuma a shekarar 2015 ta nuna kusan 'yan matan 3,000 ne wannan haramci ya shafa, wasu na hasashen adadin ka iya karuwa sosai.
Duk da cewa an kafa cibiyoyin karatu kashi biyu, da nufin samar da wata hanya ta ci gaba da bai wa ƴan mata masu juna biyu da masu shayarwar damar samun ilimi, suna halarta ne sau uku kacal a mako kuma darussa hudu ake koya musu; kotun ta ECOWAS ta yanke hukunci a shekarar 2019 cewa ''hakan ma wani salo ne na nuna wariya'' inda ta umarce su da su dakatar.
Manufar hakan ga duka wadannan 'yan mata ita ce, an cire su daga zaman zana jarrabawar (BECE), da ake bukata don shiga makarantun sakandare ko sauran manyan cibiyoyin karatu na gaba da sakandare da kuma (WASSCE), da ake bukata wajen samun shiga jami'oi da manyan makarantun gaba da sakandare masu muhimmanci wajen samun ayyukan yi.
"Mun gaza game da wadannan 'yan mata,'' in ji Hannah Fatmata Yambasu, ta Kungiyar mata masu fafutukar hana cin zarafi da ci da gumin kananan yara a kasar Saliyo (WAVES) daya daga cikin kungiyoyin da suka kai gwamnati kotu don ta janye haramcin.
"Hankalin kowa ya koma kan shawo kan matsalar Ebola kuma bamu fahimci ta'asar da ake tafkawa kan kananan 'yan matan ba. Amma mun koyi darasi.
Mun fada wa 'yan matan ba za mu yi watsi da su a wannan lokaci na annobar cutar korona ba."
Sauya tunani da halayyar mutane
Wannan karon abubuwa sun sauya sosai saboda gwamnati ta fahimci matsalar. A bara ne shugaba Julius Maada Bio ya ayyana fyade a matsayin wata babbar matsala ta kasa, ya kuma yi alkawarin daukar matakai.
Ministan ilimi David Moinina Sengeh, bayan dage haramcin a watan Maris da ya gabata, ya albishir kan abin da ya kira sabon sauyi na ''saka tsauraran matakai'' wanda aka ''karfafa guiwa da tallafa wa duka yara su fahimci 'yancinsu na samun ingantaccen ilimin bai daya, ba tare da nuna wariya ko bambanci ba''.
A karon farko, 'yan mata masu juna biyu kusan 1,000 ne suka samu zauna rubuta jarrabawarsu.
Don haka, a ganin Hannah da kungiyoyi kamar WAVES, fafutukar ba wai game da sauya tunani da halayyar shugabannin kasar bane kawai, har ma a tsakanin al'umma ita kanta.
Haramta wa 'yan mata masu dauke da juna biyu zuwa makaranta ya zama ruwan dare a kasar ta Saliyo. Lokacin da aka dakatar da haramcin cikin watan Maris, wata mata ta shaida wa wakilin BBC Umaru Fofana cewa ba za ta ''amince 'yarta ta zauna a aji daya da wata mai juna biyu ba - hakan ba tarbiyya mai kyau ba ce''.

Asalin hoton, Waves
Iyayen Fatu Francis da Iye na farin ciki cewa 'yarsu za ta ci gaba da zuwa makaranta yayin da take dauke da juna biyu. Sun ce janye wannan haramci ya sauya tunaninsu game da batun, kuma fatansu a yanzu shi ne su ga Fatu ta samu ilimi, da ba don haka ba da tuni sun yi mata aure tun a shekarar bara.
Amma sun ce an samu bambance-bambancen ra'ayoyi ne daga karamin yankinsu a Nyawa Lenga a gundumar Bo.
"Wasu sun yi na'am da matakin namu na kai kuka game da [cin zarafin] 'yar tamu zuwa kungiyar WAVES da kuma 'yansanda don dakatar da maza daga cin zarafin 'yayanmu mata,'' sun shaida wa BBC cewa, yayin amsa tambayoyin da kungiyar WAVES ta ba su.
"Amma wasu ba su amince da matakin 'yarmu ta rika zuwa makaranta ba a irin yanayin da take ciki''.
Ita kanta Fatu ta ce rayuwar ta kasance mai wahala a makarantar. Ta yi bakin kokarinta amma duk da haka ta kasa sakin jikinta ta zauna na tsawon lokaci ta yi karatu, don haka ta ce ''Na kan halarci daukar darussan amma ba a koda yaushe ba''.
Kawaye "sun daina kira na zuwa wajen wasannin motsa jiki da suran harkoki, musamman lokacin cin abincin rana, saboda sun ce ba zan iya tabuka komai ba''.
Amma ta kara da cewa: ''Ina so in ci gaba da zuwa makaranta idan na haihu saboda ina so in kammalla makaranta in zama mai ilimi.
"Ina fatan in zama ma'aikaciyar jinya nan gaba. Idan na girma ina so na ga na zama abin koyi ga sauran 'yan mata da mata.''
Makarantarta ta ce tana da jan aiki a gabanta na sauye-sauye saboda janye wannan haramci, a aikace da kuma a halayya. Shugabar makarantar ta fahimci cewa wasu daliban ''na nuna kyama da wariya'' ga Fatu, ta kuma tabbatar da cewa wasu malaman kan nuna ''halayyar da bata dace ba'' kan yadda take tafiyar ta karatunta a cikin aji.
Amma kuma, ta gano cewa wasu dalibai 'yan mata masu shayarwa da suka dawo makaranta suna nuna cewa suma yanzu sun zama manya tun kafin lokacinsu ya yi, kana ''suna yin abubuwa kamar su manya ne … kuma a wasu lokuta suna yi wa malamansu rashin kunya''.
Da makarantar da iyayen Fatu har ila yau sun shaida wa BBC ta hanyar tambayoyin ta kungiyar WAVES ta aike mata cewa, ana bukatar ingatattun ma'aikatan kiwon lafiya da hadin guiwar makarantar don tabbatar da cewa ita da sauran 'yan matan da ke cikin hali irin nata su kasance cikin koshin lafiya, ba jariransu kadai ba, amma har ta yadda za su iya gudanar da ayyukan su na makaranta.
Tsattsauran matakin da Tanzania ta dauka
Yanzu kungiyar 'Equality Now', da ta shige gaba wajen kai kasar Saliyo gaban kotu, yanzu fadan nata ya kai ga kasar Tanzania.
Ta gabatar da karar ne a watan da ya gabata a kotun Afrika kan kare haƙƙin bil adama, cike da fatan ganin an janye haramci kan hana 'yan mata masu juna biyu halartar makaranta a kasar ta yankin Afrika ta Yamma.
Amma kuma, Judy Gitau ta kungiyar 'Equality Now' ta ce batun na kasar Tanzania daban ne da na kasar Saliyo, don haka babu tabbacin samun sakamako iri daya.
"A kasar Saliyo, manufofin wadanda aka gada ne, kuma ba a saka batun shugabanci a ciki ba , ta ce.
"Amma, yayin da sauran kasashen suka kauce wa yin wannan haramci, an tursasa shugabanci a Tanzania da gangan a cikin shekarun baya-bayan nan.''
Tana misali ne da gargadin Shugaba John Magafuli na shekarar 2017: '' Muddin ina shugabancin kasa, babu wata mai juna biyu daliba da za a amince ta koma makaranta. Bayan samun ciki , babu sauran wani abu''.
An yaba masa a lokacin da ya bayyana haka a wani taron gangami a wajen birnin Dar es Salaam: "Idan muka bari wadannan 'yan mata suka koma makaranta, wata rana za mu wayi gari duka 'yan matan na komawa gida don su bai wa jariransu nono." Ya kuma yi barazanar yanke hukuncin daurin shekara 30 ga mazan da suka yi wa 'yan matan ciki.

Asalin hoton, Getty Images
Tanzania na da rabin adadin kananan 'yan mata masu juna biyu a duniya.
Kamar yadda hukumar kididdigar yawan al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ta bayyana, a shekarar 2016, daya cikin kananan 'yan mata hudu tsakanin shekaru 15 zuwa 19 suna da juna biyu ko kuma sun haihu.
Bayanan gwamnati ita ma a shekarar 2016 ya nuna kashi 36 bisa 100 na mata an yi musu aure ne kafin su kai shekara 18.
Bankin Duniya, wanda ya bai wa kasar ta Tanzania bashin Dala miliyan 500 kwatankwacin Fam 370 a wannan shekarar, ya ce rabi daga cikin dalibai dubu 60 da suka bar makaranta a kowace shekara 'yan mata ne, wanda kimanin 5,500 sun bari ne saboda suna da juna biyu.
Tanzania ta yi la'akari da matsalar kuma ta bullo da wasu tsare-tsare da ayyuka a makarantu don samar da karin ilimin jima'i da kiwon lafiya.
Ta kuma bayar da muhimmanci kan samun damar ilimin sakandare a wani bangare na bashin Bankin Duniya.
Amma Ms Gitau ta ce, wannan bai kai ga yadda zai wadatu wajen tabbatar da cewa duka 'yan matan sun samu ilimi ba.
Kuma ta musanta batun al'adar cewa, barin 'yan mata masu juna biyu zuwa makaranta zai gurbata tarbiyyar sauran 'yan matan.
"Muna ganin cewa zai nuna wa 'yan matan matsala da nauyin da ke tattare da daukar ciki, zai zama wani darasi ga sauran …su fahimci 'yancinsu na kula da lafiyar jikisu.''
Mujallar kiwon lafiya ta Lancet a kasar Birtaniya ta yi nazari kan kasashen Afrika tara da suka janye haramci kan komawar 'yan mata makaranta a tsakanin shekarar 1993 da 2015.
Ta gano cewa kididdigar adadin yawan 'yan matan masu dauke da juna biyu 'yan shekara daga 14 zuwa 20 ya ragu bayan da aka janye haramcin.
Wani mai sharhi ya kuma bayyana cewa rashin ilimin 'yaya mata ba kawai yana haifar da koma baya ga fannin tattalin arzikin iyayensu bane.
Hukumar UNFPA ta fitar da rahoton cewa kasar Tanzania ka iya asarar fiye da dala biliyan biyar a ko wace shekara saboda yawan adadin 'yan matan da ke barin makaranta.
Kungiyar 'Equality Now' ta shafe fiye da shekara uku tana fafutikar ganin gwamnatin Tanzania ta janye haramcin, ba tare da samun nasara ba, don haka kai kara zuwa kotun Afrika ita ce mafita ta karshe.
"Tsare-tsaren hukuncin shari'ar ka iya daukar shekaru,'' in ji Ms Gitau. "Mun kai wannan matsayin ne bayan tsawon lokacin da aka dauka, duk da cewa muna cike da fata saboda 'yan matan ba zai dau tsawon lokaci ba.''











