Katsina: 'Yan sanda sun ceto ɗaliban Islamiyya 80 da aka yi garkuwa da su a jihar

Rundunar 'yan sandan Jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya ta tabbatar da ceto 'yan makarantar Islamiyya 80 da ɓarayin mutane suka yi yunƙurin sacewa ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Funtua.

A cewarsa ɓarayin, sun sato mata huɗu a ƙauyen Dan Baure da ke yankin, inda a hanyarsu suka haɗu da 'yan Islamiyyar da a kan hanyar komawa gida daga wurin Maulidi.

"Ɗaliban na Hizburrahim Islamiyya da ke Mahuta guda 80, sun fito ne daga wurin Maulidi da aka yi a Unguwan Alkasim da ke Dandume sai barayin suka hada su da mutum hudu da suka sato da shanu 12," in ji ASP Isa.

"Daga nan wasu suka rugo suka ba mu labarin abin da yake faruwa sai muka tura jami'anmu da haɗin gwiwar sojoji da 'yan ƙato-da-gora suka yi ba-ta-kashi da ɓarayin."

A cewar kakakin 'yan sandan, lamarin ya yi sanadin mutuwa da kuma jikkatar ɓarayin "kodayake har yanzu ba mu san adadinsu ba".

"Amma kwamishinan 'yan sanda ya tura ƙarin jami'ai yanzu da safen nan domin kirga waɗanda suka mutu. Mu dai a ɓangarenmu babu wanda ya mutu."

Lamarin na faruwa kwana biyu bayan sakin 'yan makarantar sakadaren maza ta Kankara guda 344 da aka sace a jihar ta Katsina a makon jiya.

Sace su ya ja hankalin duniya a kan matsalar rashin tsaro da ke ta'azzara a arewa maso yammacin Najeriya.