Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya shirin ciyar da 'yan makaranta a Kano
Ka iya latsawa domin sauraron wannan shirin
A wani yunkuri na cika alkawuran da ya dauka, jim kadan bayan hawansa mulki a shekara ta 2016, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin ciyar da yara 'yan makaranta a matsayin wani bangare na shirin bunkasa walwalar al'ummar kasar.
Sai dai 'yan shekaru bayan kaddamar da shirin, an rinka kokawa kan yadda ake gudanar da shi, daga bisani kuma shirin ya tsaya cik, bayan bullar cutar korona, abin da ya sa aka rufe makarantu manya da kanana a fadin kasar.
Sai dai dakatar da shirin, wanda ya bayyana karara bayan bude makarantu a kasar, ya zo da tasa illar, inda yake kokarin karya kwarin gwiwar wasu dalibai, har ma da malaman makarantun.
Haruna Ibrahim Kakangi ya je jihar Kano, inda ya duba mana wannan matsala, ga kuma rahoton da ya hada mana, wanda zai zo muku a matsayin daya daga cikin jerin rahotanni na musamman da BBC Hausa ke kawo maku tare da tallafin gidauniyar MacArthur.