Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
GSS Kankara: Abubuwan da Buhari ya gaya wa daliban da aka ceto
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana ɗaliban makarantar Kankara a Katsina bayan kuɓutar da su daga ƴan bindigar da suka sace su.
Shugaban ya gana da ɗaliban a fadar gwamnatin Katsina kwana guda bayan ceto ɗaliban su sama da 340.
An kubutar da ɗaliban ne yawancinsu yara ƙanana a ranar Alhamis bayan shafe kusan tsawon mako ɗaya a daji a hannun masu garkuwa da su.
Shugaban ya jinjinawa gwamnatin Katsina da kuma sauran waɗanda suka taimaka aka kuɓutar da ɗaliban.
Shugaban ya fara yin jawabin ne da yin kira ga ɗaliban su saurare shi kuma su fahimce shi.
Ya yi kira ga ɗaliban su ƙara himma ga neman ilimi su manta da abin da ya same su, tare da cewa sun yi sa'a ba su sha wahala ba.
"Wannan ƴar guntuwar wahalar da kuka sha ku bar ta a baya ku ci gaba ku mayar da hankali ga karatu a wannan makaranta da kuke ciki ta ilimin kimiyya ku mayar da hankali," in ji Buhari.
Shugaban ya kuma shaida wa ɗaliban cewa ilimin kimiyya da suke karatu a makarantarsu shi ne na zamani, a cewarsa "ba wanda ya karanci Tarihi ko Turanci ba, waɗanda suka yi kimiyya su ne za su fi samun aiki a nan gaba."
Shugaba Buhari ya kuma ce matsalar makiyaya da manoma tsohon rikici ne tun kafin ya shiga aikin soja inda ya bayar da misali da mutanen Filato da ya ce abokan wasan Fulani ne kuma da ke kukan cewa, "masu kiwon shanu suna masu fitina a gonaki."
Wannan abin ya girme ni, kusan a jiya na cika shekara 78, cikinsu, shekara ta tara daga inda kuke a nan a Katsina na yi na shekara bakwai a Kafin Soli, shekara ɗaya a Kankia," kamar yadda shugaban na Najeriya ya shaida wa ɗaliban Ƙanƙara.
Dalilin zuwa gonar Buhari
Buhari wanda ya rage masa shekaru kusan biyu da rabi ya sauka ya kuma faɗa wa ɗaliban dalilin da ya sa yake ziyartar gonarsa.
Ya ce ya yi rantsuwa da Kur'ani zai tsare kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma dole ranar 29 ga watan biyar 2023 ya sauka ya dawo gida.
"Shi ya sa nakan zagayo na je na ga gonata da dabbobina don nasan idan Allah ya min tsawo rai a nan zan dawo - kamar yadda ake cewa karshen alewa kasa," in ji shi.
Sai dai saɓanin kiran da ƴan Najeriya suka daɗe suna yi wa shugaban na neman a tuɓe manyan hafsoshin sojin ƙasar, shugaban ya ce su ci gaba da aiki tsakani da Allah.