Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Satar mutane a Najeriya: Yaya munin lamarin yake?
Kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Afirka ta Yamma ta Boko Haram ta ɗauki alhakin sace ɗaruruwan yara ƴan makaranta a arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan harin na baya-bayan nan da aka kai makaranta a jihar ta Katsina ya haifar da tambayoyi game da tasirin Boko Haram a arewa maso yammacin Najeriya, da kuma ikon da jami'an tsaron ƙasar ke da shi na ci gaba da riƙe madafun iko a arewacin ƙasar.
A cikin shekara 10 da suka gabata, mayaƙan Boko Haram sun fi yin ta'adi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, galibi a Borno da jihohin da ke makwabtaka da ita.
A shekarar 2014 ne ƴan Boko Haram suka sace wasu darururwan ƴan mata ɗalibai daga makarantar Chibok a jihar Borno, wanda da yawa daga cikinsu har yanzu ba a gansu ba. Haka kuma an sake yin garkuwa da yara 'yan makaranta a shekarar 2018 a Yobe, jihar da ita ma ke arewa maso gabas.
Ana danganta rashin zaman lafiya a yankin arewa maso yammacin Najeriya da ayyukan ƙungiyoyin da ba a bayyana su ba, waɗanda galibi ake kira da ƴan fashin daji, da ke satar shanu da garkuwa da mutane.
Yanzu haka akwai fargabar cewa kungiyar Boko Haram na faɗaɗa ikonta.
"Abin da ba a taba gani ba shi ne al'amari mai girma irin wannan" in ji Jacob Zenn, editan mujallar cibiyar da ke bibiyar al'amuran ta'addanci ta The Jamestown Foundation Terrorism Monitor.
Mista Zenn ya ce "Da alama wani yanki ne na hada-hadar 'yan ta'adda, sannan wurin shirya dabarunsu, tare da haɗin kan Boko Haram da kuma kafa aƙidar shugabanta Abubakar Shekau."
Shi dai gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya dage kan cewa 'yan fashi ne suka sace yaran.
A lokacin da ya kai ƙololuwa a kusan shekara ta 2012, tasirin ƙungiyar ya faɗaɗa daga arewa maso gabashin Najeriya inda ya kai har maƙwabtan kasashen Nijar da Chadi.
Ko da yake kungiyar a yanzu tana riƙe da ƙananan yankuna, amma tana ci gaba da kai hare-hare duk da ikirarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa "an karya lagon ƙungiyar."
"Hare-haren ba baƙon abu bane. Yawan wadanda abin ya shafa ne abin da ba a taɓa gani ba," in ji Nkasi Wodu, wani mai kokarin samar da zaman lafiya da kuma kare hakkin dan adam da ke zaune a Najeriya.
"Duk 'yan Boko Haram da' yan fashin da ke arewa maso yamma da arewa maso gabas suna gudanar da ayyukansu ba tare da wani shamaki ba''.
Hakan ya haifar da kiraye-kiraye na yin garambawul ga yadda gwamnati ke tunkarar tsaro.
"Ta yaya mutum zai iya bayanin yadda mutanen nan ke samun damar yin tafiya a kan daruruwan ababen hawa ba tare da an gansu ba?, in ji Sarkin Musulmai na Najeriya.
"Ina batun tattara bayanan sirri da har aka gaza bankado shirinsu aiwatarwa? Yana magana ne kan sabon harin da aka kai a Katsina.
Yankin arewa maso gabas ya daɗe da zama cibiyar tashe-tashen hankula a arewa, har yanzu haka lamarin yake kan batun mace-mace sakamakon tashin hankali ya ƙaru a wannan shekarar.
Ƙaruwar mace-macen galibi na da nasaba da nasarar kwanton ɓaunar da ake yi wa sojoji.
Har ila yau arewa maso yamma ma na fama da ƙaruwar tashin hankali.
A cikin 'yan shekarun da suka gabata, musamman jihohin Zamfara, da Katsina da Kaduna an samu karuwar adadin mace-macen da ke da nasaba da kungiyoyi masu dauke da makamai da rikicin siyasa.
Dalilan da suka haifar da rashin zaman lafiya a yankin suna da sarƙaƙiya.
Wani rahoto da kungiyar International Crisis Group ta wallafa a farkon wannan shekarar ya ce "tashin hankali ya samo asali ne daga gasa kan albarkatu tsakanin makiyaya wadanda akasarinsu Fulani ne kuma da manoma Hausawa.
Abin ya ta'azzara ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar aikata laifuka, ciki har da satar shanu, satar mutane don neman kudin fansa da kuma farmakin kauyuka."
An kuma bayar da rahoton cewa kungiyoyin masu ikirarin Jihadi suna neman yin amfani da mummunan halin tsaro da ake ciki don cimma manufofinsu.
"A shekarar da ta gabata an yi mubaya'a sosai ga shugaban kungiyar Boko Haram Shekau a arewa maso yammacin Najeriya, kuma shi kansa ya amince da hakan" in ji Mista Zenn.
Wadanne dabaru sojojin ke amfani da su?
Dabarun sojojin Najeriya sun fi mayar da hankali kan kai hare-hare ta sama, don samun sansanonin mayaƙa masu nisa.
Shafin Tuwita na rundunar sojin Najeriya suna sanya bidiyo da hotuna, suna da'awar cewa suna samun nasarar kawar da kungiyoyin 'yan fashi.
Ana guje wa ayyukan ƙasa saboda babban asarar rayukan da suke yi.
Babbar matsalar dai ita ce rashin yarda da jama'a da jami'an tsaro ke yi.
"Game da hare-haren 'yan fashi, al'ummomi da yawa suna kokawa kan cewa lokacin da suka kai rahoton yiwuwar kai musu hari zuwa ga sojoji ko ƴan sanda ba a kawo musu wani ɗauki. Wannan ya haifar da rashin yarda da jami'an tsaro," in ji Mista Wodu.
Masu sharhi kan al'amuran tsaro sun ce wannan dabarar ta sa manyan biranen sun kasance masu tsaro, amma yankunan karkara na cikin rauni.