Makon bikin nuna kayan ƙawa a birnin Dakar na ƙasar Senegal: Tafiyar rangwaɗa a tsakanin bishiyoyin kuka

Group shot of models

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Masu shirye bikin makon nuna kayan ƙawa na wannan shekarar a birnin Dakar na da saƙo ga duniya: ɗorewar abu ya danganta ga tsari mai kyau.

Bayan da dokokin korona suka tilasta musu yin bikin a waje, masu adon nuna kayan ƙawar sun hallara a ƙarƙashin bishiyar kuka domin yin nunin tafiyar rangwaɗa.

Bikin, wanda aka gudanar a ƙarshen mako a babban birnin ƙasar Senegal, da aka yi wa taken ɗaukar ɗawainiya game da muhalli, ya samu halartar masu zayyana kayan ƙawa 20 waɗanda kayayyakinsu - da aka baje a bakin hanya da kuma waɗanda ake sayarwa a shaguna - an ɗinka su da hannu ne, a maimakon yadda ake ɗinka su da yawan gaske a masana'antu.

Models queuing up

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

"Masu zayyana kayan ƙawa da dama na yin wani abu da ake kira "rashin yin gaggawa wajen ɗinka kayan ƙawa" amma ba su sani ba,'' in ji Adama Ndiaye, wacce ta ƙirƙiri makon bikin nuna kayan ƙawa na birnin Dakar, kuma mai zayyana kayan ƙawa na Adama Paris.

"An yi su ne a anan, kana ba a yi su da yawa ba. Mun shafe shekaru muna jin kunyar hakan amma kuma yanzu muna alfahari da hakan. Wannan abu ne mai asalin kyau."

Two models

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

A wani abu da muke kira "ɗinka kayan ƙawa na gaggawa", masu saye, waɗanda galibi daga yammacin duniya suke, na saye tare da zubar da kayan ƙawa da yawan gaske, da ke haifar da ƙaruwar gurɓatar muhalli mai nasaba da masana'antu.

Adadin yadda ake samun tufafin da ke lalacewa kafin a zubar ya ragu da kashi 36 bisa ɗari a cikin shekaru 15 da suka gabata, kamar yadda wani rahoton ƙungiyar Ellem Macarthur Foundation na shekara ta 2017 ya bayyana.

A kowace shekara sarrafa tufafi da rinin yaduka na lashe kusan tan miliyan ɗari na irin kayayyakin ciyar da masana'antun da ba za a iya sabuntawa ba, kana yakan fitar da gurɓatacciyar iska, kamar yadda rahoton ya bayyana.

People getting ready

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

A shekara ta 2015 kaɗai, adadin gurɓatacciyar iskar gas ta carbon da ke fita daga masana'antun sarrafa tufafi kaɗai ya kai fiye da na wanda ke fita daga jiragen sama na ƙasa da ƙasa da kuma na ruwa idan aka haɗa.

Haka kuma, gurɓatattun sinadaran da ke fita daga wurin da ake rina tufafin na haifar da kashi 20 bisa ɗari na gurɓacewar ruwa a faɗin duniya.

Akasarin yadukan da aka yi amfani da su a bikin makon nuna kayan ƙawa na Dakar a wannan shekarar, duk da cewa an haɗa su a Afirka, amma an shigo da su ne daga ƙasashen waje musamman Turai da kuma China.

Composite of two models

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

1px transparent line
Shadows on a tree

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

"Ba komai ne muke sarrafawa a nan ba, don haka ba za mu iya zayyana kayan da asalinsu kashi ɗari bisa ɗari ba ne na Senegal," in ji Ndiaye, wanda ke shigo da kayan aiki daga ƙasar Thailand.

"Amma duk da haka mun yi ƙoƙari wajen yin wasu abubuwa."

Baobab forest

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Bikin na ranar Asabar, wanda ya yi la'akari da alkinta muhalli, an yi shi ne a filin da ke cike da bishiyoyin kuka.

Amma kuma, yanayin wurin ya kasance cike da ruwan sha na cikin robobi da kuma lemuka, tabarmi da manyan hotuna ɗauke da tambarin ruwan roba na kamfanin Kirene, wanda ya ɗauki ɗawainiyar bikin.

Models sitting on the floor

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Robobin ruwan kamfanin Kirene, sanannu ne a kan titinan birnin Dakar har da gaɓar teku, inda tarin dattin robobin ruwa suka mamaye.

Amma kuma Ndiaye ta ce tana buƙatar taimakon kuɗi, kuma kamfanin ya yi alƙawarin ƙirƙiro wani shiri da za a riƙa sabunta amfani da robobin ruwan da aka jefar.

"A gani na, samun damar yin magana a kan ɗorewar abu dole ina buƙatar taimako, saboda hakan yana cin kuɗi," in ji ta.

Model wearing dark clothes

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

Bel Jacobs, daya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiru ƙungiyar sa ido kan dokar makon nuna kayan ƙawar, ya ce ya kamata a jinjina wa bikin makon wajen yin la'akari da bayar da muhimmacin tattaunawa kan ɗorewar shirin.

Ƙungiyar ta Jacob ta yi ƙaurin suna wajen jajircewa da kuma yin zanga-zanga kan a soke makon nuna kayan ƙawa na birnin London.

2px presentational grey line

Wasu ƙarin labaran da za ku so ku karanta:

2px presentational grey line

Ta ce: "Ana gudanar da makonnnin bikin nuna kayan ƙawa ne don bunkasa yadda za a ci gaba da sayen sabbin tufafi," . "Za su cigaba da kasancewa bukukuwan nuna fasaha, ta amfani da tunani mai zurfi da aka ƙirƙira.

Jacobs ta yi nuni da bikin makon nuna kwayan ƙawa na Copenhagen, inda ake buƙatar samun amincewa ƙa'idoji 17 na ɗorewar shirin nan da shekara ta 2023 domin samun cancantar gudanar da bikin.

Sun haɗa da amfani da kashi 50 bisa ɗari na kayayyakin da aka sake sabunta amfani da su, da yin alƙawarin ba za a lalata kayyakin da ba a sayar ba, da kuma amfani da jakukunan zuba kayan da ba za su gurɓata muhalli ba.

Model in a red dress

Asalin hoton, Annika Hammerschlag

1px transparent line

Rubutu da hotuna daga Annika Hammerschlag