Sulaiman Panshekara: An ɗaura auren matashi ɗan Kano da Ba'amurkiya
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon ɗaurin auren
Hausawa kan ce rana ba ta ƙarya... yau Lahadi, 13 ga Disamban 2020 aka ɗaura auren matashin nan ɗan Jihar Kano wato Isa Sulaiman Panshekara mai shekara 26 da sahibarsa Ba'amurkiya.
Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Tsakiya, shi ne waliyyin amarya Janine Sanchez.
Ɗumbin mutane ne suka taru a masallacin Jumma'a na Gasau da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, domin shaida ɗaurin auren da aka jima ana dako, bayan shafe tsawon lokaci suna shan soyayya.
Matashin ya biya zunzurutun kuɗi har Naira Dubu 50 a matsayin sadaki lakadan ba ajalan ba.
Mahaifin ango Mallam Sulaiman, ya shaida wa BBC cewa ya amince a ɗaura auren ne bayan amincewa da dukkanin sharuɗɗan da ya gindaya kafin ya bayar da ɗansa.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci ɗaurin auren har da Sanata Shehu Sani, tsohon Sanata mai wakilar jihar Kaduna a Majalisar Dattawa ta Najeriya, da kuma shugaban ƙaramar hukumar ta Kumbotso.
Abin jira a gani shine lokacin da Ango zai bi Amarya, duba da cewa jim kaɗan bayan ɗaura aure uban ango ya ce ɗansa zai ci gaba da zama da shi, sai dai kuma shi angon ya ce za a jira ne zuwa lokacin da za a kammala tattara takardu.
Masoyan dai sun fara haduwa ne ta shafin Instagram a shekarar da ta gabata.
"Mun fara ne bayan da na nuna sha'awar kasancewa daga cikin masu bibiyarta a shafin Instagram sannan idan ta wallafa hoto a shafinta ina danna alamar so wato liking."
"Bayan wani dan lokaci sai na lura akwai wasu 'yan damfara ta intanet da suke kokarin damfararta, sai na ankarar da ita kuma hakan da na yi ya burgeta har take cewa ni mutum ne mai gaskiya. Abin da na yi shi ne ya janyo hankalinta gare ni. "
"Daga nan muka fara aika wa juna sakonni har da kiran bidiyo kuma hakan ne ya kai mu ga inda muke a yanzu."
Isa ya ce iyayensa sun amince ya auri masoyiyar tasa Janine kuma nan da watan Maris za a yi bikinsu inda za su wuce Amurka.
"Bayan bikinmu a watan Maris idan Allah ya yarda, Amurka za mu wuce inda nake fatan samun aiki na koma makaranta sannan samu kungiyar da zan rika buga wa kwallo."













