Dalilan da ke sa manya yin fitsarin kwance

Matsalar fitsarin kwance

Asalin hoton, Getty Images

Ga yawancin manya ko magidanta abu ne mai wahala su fito su bayyana cewa suna fama da matsalar fitsarin kwance saboda lalura ce da aka fi alaƙalantawa ga yara ƙanana.

Bincike ya nuna cewa ana samun kashi biyu cikin 100 na manya da ke fama da matsalar fitsarin kwance.

Dr Salihu Kwaifa ƙwararren likita a babban asibitin Wuse da ke Abuja ya ce yara sukan kai shekara biyar har zuwa 10 suna fitsarin kwance, kuma ga yara ba ciwo ba ne alama ce ta girma

Likitan ya ce a duk lokacin da aka ga babba wanda ya haura shekara 18 yana fitsari to rashin lafiya ce.

Ga waɗanda ke fama da matsalar fitsarin kwance an fi son su ziyarci likita domin gaggauta magance matsalar.

Shafin lafiya na WebMd ya bayyana cewa matsaloli da dama ne na lafiya ke haifar da fitsarin kwance ga manya da suka da haɗa da matsala ga mafitsara ko damuwa ko kuma shan wani magani.

Abubuwan da ke sa manya yin fitsarin kwance

Dr Salihu Kwaifa ƙwararren likita a babban asibitin Wuse da ke Abuja ya bayyana abubuwan da ke sa manya yin fitsarin kwance kamar haka:

Ƙwayoyin cuta da suka wuce ko wata matsala ta wani sinadari da ke tare yawan fitsari ko ƙarantarsa na iya sa mutum fitsari a kwance.

Ciwon sikari da ake kira diabetes yana sa yawan fitsari wanda zai iya sa mutum yin fitsarin kwance saboda yana yawan sa yawan fitsari da kuma sa mutum dinga shan ruwa.

Magidanci na iya samun matsalar fitsarin kwance idan yana da matsalar mafitsara da yakai ba ya iya riƙe fitsari.

Akwai kuma nau'in ciwon da ke addabar hanyar mafitsara wanda zai iya sa babba yin fitsarin kwance.

Haka kuma babba na iya samun matsalar fitsarin kwance idan ya samu bugun ƙwaƙwalwa ko ciwon mantuwa.

Akwai kuma wasu magungunan da idan mutum ya sha da ke yawan sa fitsari za su iya sa mutum yin fitsari a kwance.

Ga mata kamar waɗanda mahaifarsu ta zazzalo, za su iya samun matsala ta fitsarin kwance.

Haka ma ga masu yawan shan ruwa har cikin dare idan za su kwanta ko idan sun farka bacci za su iya yin fitsarin kwance.

Shin fitsarin kwance ga manya matsalar aljanu ce?

Matsalar fitsarin kwance

Asalin hoton, Getty Images

A al'adance matsalar fitsarin kwance ga wanda ya manyanta ana danganta shi da iska ko kuma aljannu.

Kuma duk wani ciwo da ba a san ƙimarsa ko makarinsa ba an fi alaƙanta shi da iska.

Amma Dr Kwaifa ya ce fitsarin kwance ga manya ciwo ne wanda idan an bincika za a gano, ba ya da wata alaƙa da iska ko aljannu.

"Duk wani ciwo da aka bincika za a gano yana da musabbabi," in ji likitan.

Wasu hanyoyin da za su taimaka

Ga wadanda ke shan maganin da ke sa su yawan fitsari za su iya daina shan maganin.

Sannan ana iya koyawa mafitsara yadda za ta riƙe fitsari musamman idan lokacinsa bai yi ba.

Akwai magungunan da ake bayarwa a likitance da za su hana yawan fitsari, waɗanda kuma za su daƙile fitsarin kwance.

Ga wanda ke fitsarin kwance zai iya ƙauracewa shan ruwa a lokacin kwanciya.

Mutum zai iya amfani da agogo ya sa alam domin saita lokacin tashi yin fitsari a cikin dare