An ta yin jefe-jefe a majalisar dokokin Taiwan kan shigo da naman alade daga Amurka

'Yan majalisar dokokin Taiwan na jifan juna da hanjin alade

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rikicin da ya ɓarke a majalisar ba wani abin mamaki ba ne a Taiwan

'Yan hamayya a majalisar dokokin Taiwan sun yi ta naushin juna tare da jifan juna da hanjin alade a zauren majalisar dokoki lokacin da ake tsaka da neman a sassauta dokar shiga da naman alade daga Amurka.

Sun ce wannan mataki na gwamnati na barazana ga 'yan ƙasar ganin cewa yana dauke da wani magani da aka haramta amfani da shi a jikin naman alade a Taiwan da Tarayyar Turai saboda yana da illa ga lafiyar mutane.

Jam'iyya mai mulki ta musanta wannan zargi tana kiran a koma kan kujera domin ci gaba da mahawara.

'Yan majalisar dokokin Taiwan sun saba tafka rikici.

'Yan majalisar daga jam'iyyar adawar Taiwan ta (KMT) sun jefa bokitai cike da hanjin alade kan shugaban majalisar Su Tseng-chang a ranar Juma'a domin hana shi tambayoyi a majalisar.

Wasu kuma suka yi ta naushin juna a ƙoƙarin dakile jifan da 'yan majalisar KMT ke yi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

An ruwaito jam'iyyar adawa ta DPP ta yi alawadai da wannan ƙazanta, tana cewa wannan wulaƙanta abinci ne, tana mai cewa kamata ya yi a ƙara komawa kan teburin mahawara.

Pigs intestines on parliament floor

Asalin hoton, Reuters

Amurka ta yi marhaba da wannan matakin da shugaba Tsai Ing-wen ta ɗauka a watan Agusta na sassauta haramcin shigowa da naman alade daga Amurka daga ranar 1 ga watan Janairu.

Amma matakin bai yi wa 'yan adawa daɗ ba, wanda hakan ya janyo damuwa daga mutan ƙasar kan rashin aminci kan abinci bayan rikicin da ta janyo a ƙasar.

Haramcin da aka yi na kwanan nan kan amfanin da naman alade a Taiwan, da China da Tarayyar Turai, ya biyo bayan damuwar da aka nuna kan illar da naman zai iya yi wa bil adama.

'Yan majalisar Taiwan sun yi ƙaurin suna kan tayar da rikici a zauren majalisar.

An sha ganinsu suna jefe-jefe da robar ruwa wasu na janyo gashin kan juna da dai sauransu.

A wani rikici da ya fi ƙamari a 2017, yan majalisar sun yi ta jifan juna da kujeru kan wani ƙudurin gina abubuwan more rayuwa.