Rikicin Hong Kong: Kasashen duniya na gargadin China kan matakinta a kan Hong Kong

'Yan sandan Hong Kong sun kama wani mutum a yankin Causeway Bay ranar 12 ga watan Yuni

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu adawa na fargabar dokar za ta hana 'yancin gudanar da zanga-zanga

Burtaniya da Tarayyar Turai da Nato sun nuna damuwa game da dokar 'yancin kan Hong Kong da shugaban China ya sanya wa hannu mai cike da rudani, wanda zai ba ta cikakken iko kan yankin Hong Kong din.

Shugaban China Xi Jinping ne ya sanya wa dokar hannu yana cewa kuma za a kara ta a cikin dan karamin kundin tsarin mulkin Hong Kong din, tare da mayar da nuna kin amincewa da ita wani babban laifi.

Shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam, ta kare dokar tana cewa za ta cike wani wagegen gibi da ake da shi a tsarin tsaron kasar.

Wata daga cikin manyan kungiyoyin da ke rajin tabbatar da dimokradiyya ta ce, tana kokarin dakatar da dukkan ayyukanta.

Kungiyar ta Demosisto ta sanar da wannan mataki ne a shafinta na Facebook, bayan da wani fitaccen dan fafutuka Joshua Wong ya ce zai bar kungiyar, wanda a baya ya jagorance ta.

Ana sa ran China za ta yi karin bayani kan dokar anjima kadan. Babu wani kwafin dokar da aka fitar ya zuwa yanzu, kuma ko Misi Lam ta ce ba za ta iya cewa komi ba kan sharudan dokar yayin da take tattaunawa da wani kwamitin majalisar dokokin kasar.

Gwamnatin Hong Kong a wata sanarwa da ta fitar ta ce, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Talata.

Ranar laraba kuma za ta kasance ranar murnar dawowar 'yancin yankin zuwa karkashin China - ranar da yawanci masu zanga-zangar rajin dimokradiyya suka fi fita.

Wannan dokar ta China na kokarin shawo kan zanga-zangar dimokradiyya da ke kara bazuwa cikin yankin.

Masu adawa na koken cewa hakan zai tauye 'yancin da ake zayyana a cikin kundin tsarin mulkin Hong Kong, wanda aka cimma yarjejeniyarsa lokacin ba da 'yancin yankin da Burtaniya ta yi a 1997.

Akwai 'yancin fararen hula kamar 'yancin magana da damar zanga-zanga da dai sauran 'yanci na cikin hadari.

Wannan layi ne

Wanne irin mataki kasashen duniya za su iya dauka?

Sakataren harkokin wajen Burtaniya Dominic Raab ya shawarci China da ta janye daga wannan kokarin da take na mamaye Hong Kong ta kuma mutunta 'yancin al'umnar yankin.

Shugaban majalisar kungiyar Tarayyar Turai Charles Michel ya ce, "wannan yunkurin zai jefa 'yancin Hong Kong cikin hadarin gaske, kuma muna Allah-lwadai da wannan mataki."

An ta harba borkonon tsohuwa domin tarwatsa taron masu zanga-zanga a Hong Kong cikin watan Mayu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ta harba borkonon tsohuwa domin tarwatsa taron masu zanga-zanga a Hong Kong cikin watan Mayu

Gwamnan Burtaniya na karshe a yankin Hong Kong Lord Patten, ya ce wannan dokar ta kawo karshen kasa daya mai tsari biyu.

A bagare guda kuma, sakataren kungiyar tsaro ta NATO Janar Jens Stoltenberg ya ce "a bayyane yake cewa China ba ta girmama matakanmu - dimokradiyya, 'yanci da kuma tsarin doka da oda."

Japan ta kira wannan doka "Abin yin nadama" Taiwan kuma gargadi ta yi ga 'yan kasarta da su guji zuwa ziyara yankin Hong Kong.

Amurka kuwa har ta fara shirye-shiryen daukar matakin kawo karshen wata yarjejeniyar kasuwanci da ke tsakaninta da Hong Kong, wanda China ta ce za ta mayar da martani kan wannan batu daga baya.

Wannan layi ne