Makaman da China ta yi amfani da su wurin kai hari kan India

An image showing iron rods studded with nails

Wani hoto ya nuna makaman da China ta yi amfani da su wurin kai hari a iyakarta da Indiya a ranar Litinin.

Rikicin wanda aka yi a Kwarin Galwan ya sa sojojin Indiya 20 suka rasa ransu wanda haka kuma ya kawo fargaba tsakanin ƙasashen biyu.

China ba ta bayyana ko wasu daga cikin sojojinta sun ji rauni ko sun mutu ba sai dai duka ƙasashen na zargin kansu da kai wa juna hari.

Iyakar ƙasashen ba a fitar da ita yadda ya kamata ba kuma sukan shiga tsakanin juna sakamakon sauyin yanayi.

Hoton da aka fitar a ranar Alhamis ya nuna makaman a tsirarasu kuma da alama an yi su ne da rodi kuma aka saka musu ƙusoshi.

BBC ta samu hoton ne daga wani babban hafsan soji da ke kan iyakar Indiya da China wanda ya ce China ce ke amfani da irin makaman.

Wani mai sharhi kan al'amuran tsaro Ajai Shukla wanda shi ne ya fara wallafa hoton makaman a shafin Twitter ya ce rashin imani ne amfani da irin makaman wurin kai hari.

Rashin amfani da makamai a yankin kan iyakar ya samo asali ne tun a wata yarjejeniya da aka cimma wa a 1996 tsakanin ɓangarorin biyu kan haramta amfani da bindigogi ko kuma abubuwan fashewa domin gudun ƙara rura wutar rikici a yankin.

Hoton ya yi yawo matuƙa a Indiya, inda mutane da dama da ke amfani da shafukan sada zumunta ran su ya baci.

Sai dai babu wasu jami'ai ko kuma hukumomi a Indiya ko kuma China da suka ce wani abu kan wannan hoto.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu arangama ne tsakanin jami'ai a wani tsauni mai tsawon mita 4,267, inda wasu sojoji suka rinƙa faɗawa cikin kogin Galwan.

Indian army trucks move along a highway leading to Ladakh, at Gagangeer some 81 kilometres from Srinagar,

Asalin hoton, EPA

Mutuwa ta farko bayan shekaru 40

Ɓangarorin biyu sun yi ta rikici kan iyakar ƙasashen a 'yan makonnin nan, sai dai arangamar da aka yi a ranar Litinin ta zama ta farko da ta sa aka rasa rayuka masu yawa bayan shekaru 45.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba daga Indiya sun bayyana cewa sojojin China 40 suka mutu, sai dai China har yanzu bata fitar da wata sanarwa ba dangane da mutanen da suka mutu.

Akwai wasu sojoji na Indiya da ake ganin cewa sun yi ɓatan dabo.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Zhao Lijian ya bayyana cewa Indiya ta ƙetare iyakarsu har sau biyu, "sun fusata tare da kai hari ga jami'an China wanda hakan ya jawo aka samu arangama tsakanin jami'an da ke tsaron iyakokin ƙasashen biyu," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Jama'a da dama a ƙasashen biyu sun sha gudanar da zanga-zanga sakamakon irin arangamar da ake samu a yankin iyakar ta Himalaya, sai dai jami'a sun sha yin gargaɗi da kuma yunƙurin sasanci ta hanyar diflomasiyya.

Ministan harkokin wajen Indiya Anurg Srivastava ya ce ministocin ƙasashen biyu sun tattauna ta waya a ranar Laraba kan lamarin, "kuma sun cimma matsaya kan cewa za a magance abin ta hanyar da ta dace".

Wata sanarwa da gwamnatin Indiya ta fitar ta bayyana cewa dakarun China sun yi ƙoƙarin yin wani gini kan iyakar ƙasar da Indiya.

Sanarwar ta zargi 'yan China da ɗaukar wannan mataki da gangan wanda ya jawo rikici da kuma rasa rayuka inda kuma suka buƙaci China ta kawo gyara a lamarinta.