Halima Aden ta daina sana'ar nuna ƙawa saboda dokokin Musulunci

Asalin hoton, Getty Images
Ƴar Amurkar nan mai tallata kayan ƙawa Halima Aden ta ce za ta daina dukkan ayyukan tallata kayan ƙawa da take yi a bainar jama'a saboda sun ci karo da koyarwar addininta.
Halima mai shekara 23 da haihuwa ta shahara har an saka ta a shafukan farko na mujallun British Vogue da Vogue Arabia da kuma Allure.
A wani sakon Instagram da ta wallafa, ta ce bayyanar annobar korona ya ba ta sarari da lokacin da ta yi nazarin halin da t ake ciki a matsayinta na mace Musulma.
"A matsayina na mai sanya Hijabi, rayuwata ta kasance cike da ƙalubale," inji ta.
Ta kuma yi tsokaci kan batun karbar ayyuakan tallata kayan ƙawa da ta rika yi waɗanda sun saɓawa koyarwar addinin da ta ke bi: "Na ɗora wa kaina laifin damuwa da samun ayyuak ba tare da la'akari da abin da aikin ya kunsa ba."
Ta ce matsalar ta samo asali ne saboda "rashin mata Musulmi ma su haɗa kayan kwalliya da na ƙawa" a cikin masana'antar da take aiki, waɗanda za su gane sanya hijabi na da muhimmanci.
Ta sami goyon bayan 'yan uwanta mata kamar Bella da Gigi Hadid da kuma Rihanna.
An haifi Halima ne a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke Kenya, kuma iyayenta ƴan ƙabilar Somali ne kafin su koma da ita Amurka tana shekara shida da haihuwa.
Wani kamfanin ƙasa da ƙasa mai tallata kayan ƙawa mai suna IMG Models ya gano ta a lokacin tana da shekara 18 yayin da ta halarci wani bikin sarauniyar kyau na Miss Minnesota USA, inda ta kai mataki na biyu.
Ita ce mace ta farko da ta sanya hijabi a bikin sarauniyar kyau, kuma daga nan ta shahara domin irin kaya masu mutunci waɗanda kuma ba sa nuna tsaraicinta da take sanyawa.
Daga nan ta sami damar fitowa a kamfen da jerin tallace-tallacen kayan ƙawa da Fenty Beauty na Rihanna da Yeezy Brand na Kanye West.

Asalin hoton, Getty Images
A saƙon da ta wallafa a Instagram Stories, ta yaba wa Rihanna domin ƙyaleta da ta yi ta ci gaba da sanya hijabi a lokutan da take tallan kayan ƙawa.
Ta ce ta taka wasu hukunce-hukuncen addininta sau da yawa a loutan da take aikin tallan kayan ƙawa - musamman rashin yin sallah a kan lokacin da addinin Musulunci ya buƙata, ko kuma amincewa ta tallata kayan kwalliya ba tare da ta sanya hijabi ba, inda ta riƙa sanya wani abu na dabam domin ta rufe kanta.
Ta ƙara da cewa ta sha yin kuka a ɗakinta na otel bayan an kammala ɗaukar wasu hotuna na kayan da ta tallata saboda ta kasa bayyana abin da ke damunta kan batun sanya kayan da suka dace wa mace Musulma.
"A gaskiya ban ji daɗin halin da nake ciki ba," kamar yadda ta wallafa a Instagram.
A watan Fabrairun bana, ta sanar da BBC cewa: "Kunya ba ta wasu mutane keɓaɓɓu ba ne su kaɗai, ba ta wasu ƙeɓaɓɓun mata ba ne. Kunya tsohuwar al'ada ce a fagen kwalliya a duniya."











