Boko Haram: Macen da ta yi kasadar ɗaukar hotunan mutanen da ƙungiyar ta tagayyara
Ku latsa hoton da sama don kallon bidiyon:
Wata mai sana'ar daukar hoto 'yar Najeriya, Nelly Ating, ta soma daukar hotunan mutanen da rikicin Boko Haram ya tagayyara tun 2014.
Ta bayar da labarin irin mawuyacin halin da wadanda rikicin ya raba da gidajensu amma suka samu matsuguni a Yola, babban birnin jihar Adamawa, suka fada a ciki.