Shirin Mata 100 Na BBC: Kar ku bari haƙuri ya kashe ku idan ana cin zarafinku - Zahara
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wata fitacciyar mawaƙiya a Afirka Ta Kudu Zahara ta ce duk da annobar da ake fama da ita a ƙasarta, hakan bai rage yawan cin zarafin mata da ake yi ba.
A matsayinta na wacce ta taɓa fuskantar cin zarafi a lokacin da take ciin shekaru 20, ta ce saƙonta ga mata shi ne: "Ku daina yin shiru. Takaicin zai kashe ku."
Zahara na cikin mata 100 da BBC ta zaɓa a bana da suka yi zarra, kuma tana wannan maganar ne albarkacin ranar yaƙi da cin zarafin mata ta duniya.