Bidiyo: Yadda aka ƙirƙiri manhajar kai ƙara kan cin zarafi a gidajen aure da aikata fyade
Latsa wannan alamar hoton na sama domin ganin yadda ake shigar da korafin cin zarafi ta hanyar amfani da manhaja a wayar hannu.
Batun cin zarafi musamman ga 'ya'ya mata a arewacin Najeriya wani abu ne da ba kasafai ake daga shi ba ballantana har a yi wa tufkar hanci saboda al'ada.
Mazaje kan doki matansu ko zagi ko kuma nau'in kuntatawa da cin zali amma matan kan jure irin wannan yanayi sakamakon al'adar da Bahaushe ke cewa 'Aljannar Mace na karkashin mijinta'.
A kan samu yanayin da matan su ma kan ci zarafin maza duk da cewa hakan ba abu ba ne da yake faruwa yau da kullum ba.
Har wa yau, cin zarafin kananan mata musamman ta hanyar fyade batu ne da ya kamata a kwarmata domin samun dauki da bin hakkin wadda aka zalunta.
Hakan ne ya sa Khadijah Muhammad Awwal wadda lauya mai kare hakkin mata bisa hadin gwiwar wani kamfanin fasaha suka kirkiro manhajar da mutum zai iya gabatar da korafe-korafensa ba tare da wadanda ba ya son su sani sun sani ba.
Sanarwa: Mun fara wallafa wannan labari ranar 8 ga watan Nuwamba, mun sabunta shi a yau albarkacin ranar yaƙi da cin zarafin mata ta duniya.