Matan da ke alfahari wajen iya ƙira'ar Ƙur'ani
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidIyon:
A ko ina a faɗin duniya kowane yanki da yadda suke daukar batun karatun Ƙur'anin mata a bayyane.
Wasu suna ganin bai kamata mace ta dinga bayyana karatunta a fili ba sai a wajen da mata zalla suke, saboda gudun kar muryarta ta jawo hankalin wadanda ba muharramanta ba.
Amma a wasu yankunan da dama, ana bai wa mata ƙwarin gwiwa kan su dinga ƙoƙarin ƙwarewa a wannan fanni na iya karatu da rera shi.
Nusaiba tana karanta Ƙur’ani a bainar jama’a tun tana ƙarama. Yanzu tana koyar da wadanda suke so su koya irin ƙira’arta.