Wani gungun masu amfani da intanet a Kenya na yaudarar ƴan mata da zuwa wajen sharholiya

Lokacin karatu: Minti 2

'Yan sanda a Kenya na binciken wani gungun masu amfani da intanet da suke neman 'yan matan da suke zaune a gida saboda annobar korona, inda suke yaudararsu da abin da 'yan sandan suka ce gayyatar su wajen sharholiya.

Batun ya fito fili ne bayan 'yan sanda sun kubutar da wasu 'yan mata uku da suka bata a babban birnin ƙasar Nairobi.

'Yan matan uku sun shaida wa 'yan sanda cewa sun ga wasu shafukan sada zumunta da suka gayyace su zuwa wajen "pati" a birnin.

'Yan sanda sun gargadi iyaye da su ringa sanya ido sosai kan 'ya'yansu.

"Sashen binciken manyan laifuka yana sanar da jama'a cewa muna farautar mambobin wata kungiya kuma za a kama su domin fuskantar hukuncin abubuwan da suka aikata", a cewar 'yan sanda a shafin tuwitar.

A baya-bayannan kafofin watsa labaran Kenya sun ringa ba da rahoton bacewar 'yan mata - wasunsu an yi musu alkawarin aiki.

A farko wannan makon dangin wata budurwa sun wallafa wani sako a tuwita suna fargabar cewa an sace 'yarsu ko kuma anyi safarar ta.

Dangin sun ce yarinyar ta bata a Nairobi ranar Asabar bayan wasu mutane sun yaudareta cewa za su ba ta aikin tallan kayan kawa.

"Kanwata tare da wasu 'yan mata shida masu shekara 16, sun yi batan dabo," matar ta fada a cikin bidiyon.

A ranar Juma'a, 'yan sanda sun wallafa a shafinsu na tuwita cewa masu yaki da safarar yara sun kubutar da uku daga 'yan matan bakwai da aka ba da rahoton sun bata.

Sannan ana ci gaba da neman sauran, a cewar su.

Ba su dai bayyana inda aka samu 'yan matan ba ko kuma ko an kama wasu mutane.

Sashin binciken manyan laifukan ya ce gungun suna aiki ne daga birnin Nairobi kuma suna amfani da lambobin wayar da aka yi wa rijista a kasashen waje.

"Yayin da ake ci gaba da bincike muna so mu gargadi mutanen da ke amfani da annobar korona suna yaudarar 'yan mata 'yan makaranta, nan ba da jimawa ba za a kama su," a cewar sasahin a sakon tuwita da ya wallafa.

Tun da farko a watan Nuwambar 2020, kasar ta gabashin Afirka ta kara tsanananta matakan kariya yayin da cutar korona da ta sake barkewa karo na biyu ta janyo karin mace-mace da karin masu kamuwa da ita.

An hana tarukan jama'a sannan an sanya dokar hana fita da daddare. An rufe makarantu a watan Maris, sai dai an dan bude su a watan Oktoba.

Gwamnati ta ce ba za a bude makarantu ba gaba daya har sai watan Janairu.

Kenya, wacce take da yawan al'umma miliyan 53 ta ba da rahoton cewa fiye da mutum 75,000 ne suka kamu da korona, kuma mutum 1,349 suka mutu, kamar yadda alkaluman jami'ar John Hopkins suka nuna.