Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da mijinta ya kulle tsawon shekara huɗu a keji kan zarginta da maita a Najeriya
Wata mata mai suna Gladys na jinya a asibitin Orerokpe da ke jihar Delta a kudancin Najeriya, bayan mijinta ya kulle ta a cikin ɗaki na shekara huɗu.
Harrison Gwamnishu, wanda shi ne ya fallasa abin da ke faruwa, ya bayyana wa BBC yadda mijin Gladys ya rufe ta cikin wani keji a tsakar gidan sakamakon mijin na zarginta da maita.
An ceto Gladys ne a ranar Laraba daga kejin da aka kulleta a tsakar gidan, kuma an bayyana cewa a cikin kejin take bayan gida da fitsari, haka kuma biredi kaɗai ake ba ta a matsayin abincinta.
A halin yanzu dai Gladys na asibitin Orerokpe inda a nan ne take jinya tare da karɓar magani.
An rufe Gladys cikin keji
Harrison ya bayyana cewa Gladys na da 'ya'ya takwas, haka kuma ta haifi uku daga cikinsu yayin da take kulle a cikin kejin.
"Sunanta Gladys, kuma ita asalin 'yar garin Ozoro ce daga jihar Delta, kuma da alamu ta kai shekara 40. A yanzu, ba ta cikin hayyacinta da za ta iya magana domin tun jiya ba ta ce komai ba.
"Amma muna so mu kai ta zuwa wani asibiti domin duba lafiyarta. A halin yanzu mijinta na wurin 'yan sanda."
Harrison ya ƙara da cewa a halin yanzu, ma'aikatar harkokin mata ta jihar Delta na kula da 'ya'yan matar saboda ƙanana ne, tun daga babban zuwa ƙaramin.
Ya ƙara da cewa yayin da ake kula da mahaifiyar yaran kafin ta murmure, za su san yadda za a yi a kai wannan lamarin zuwa ga sashen da ke binciken laifuka a jihar wato State CID.
An kama mijin Gladys
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen jihar Delta, Onome Umukoro ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka kama mijin Gladys domin ƙaddamar da bincike a kansa.
Umukoro ya bayyana cewa mijin ya shaida musu wai matar na da taɓin hankali ne shi ya sa, kuma ana zarginta da maita, amma hakan ya sa yake tare da ita.
Ya ce ya kai ta wurin masu maganin gargajiya daban-daban amma lamarin ya gagara.
Ya kuma ce ya kai ta wurin danginta amma sun yi watsi da ita inda suka ƙi karɓarta wanda hakan ya sa ya dawo da ita gida domin ya ci gaba da huƙuri da ita.