Yadda uwa ta 'kashe' 'ya'yanta da hannunta a Kano

Rundunar 'yan sandan Jihar Kano a arewacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar wasu yara biyu da ake zargin mahaifiyarsu da aikatawa.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Sagagi Layin 'Yan Rariya da ke kwaryar birnin Kano.

Kanin mahaifin yaran da aka kashe mai suna Sadik Haruna ya shaida wa manema labarai cewa matar ta samu sabani ne da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya.

Yaran da ake zargin mahaifiyar tasu ta kashe su ne Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da 'yar uwarsa Zahra'u Ibrahim mai shekara uku kuma sun gamu da ajalin nasu ne ranar Asabar.

"Tun bayan ya yi aure ta ƙi kwantar da hankalinta," in ji Sadik. "Kuma auren nasa bai fi wata biyu ba zuwa uku."

Ya ƙara da cewa: "Ba yanka su ta yi ba amma akwai yankan wuƙa a jikinsu da sannan kuma akwai rauni a kansu, wanda shi ne ya fi yi musu illa.

"Mijin nata ba ya gidan a lokacin da abin ya faru kuma har sai da ta kira shi suka yi waya kafin ta aikata kisan".

Lamarin ya daure wa mutane da dama kai a unguwar ta Sagagi da ma fadin jihar Kano, musamman makwabtan gidan da lamarin ya faru, inda suke cewa a iya sanin da suka yi wa matar ba ta da tabin hankali haka kuma ba a san ta da shaye-shaye ba.

Sai dai wasu sun kuma alakanta abin da matar ta yi da karin auren da mjinta ya yi a 'yan kwanakin baya, wanda har ta kai ga sun samu rashin jituwar da ya janyo mutuwar aurensu amma daga baya aka daidaita su.

Ana neman matar

BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaran da aka kashe ma'ana mijin matar da ake zargi da kashe 'ya'yan natan, amma bai iya magana ba saboda yanayi na juyayi da alhali ni da ya ke ciki sakamakon abin da ya faru.

Wani lamarin da yake kara daure kai a cikin batun shi ne rashin sanin inda matar take da kuma halin da take ciki, domin a cewar kakakin rudunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa abin da suka sa gaba yanzu shi ne neman inda matar take, domin tuni suka kaddamar da bincike.

Tuni dai aka yi wa yaran jana'iza a dai-dai lokacin da ake ci gaba da neman mahaifiyarsu da ake zargin ita ta raba su da duniya, bayan ta sha wahalar daukar cikinsu da rainonsu har suka fara zama mutane.

Lamarin dai ya dauki hankulan jama'a da dama musamman ganin irin shakuwar da ke tsakanin da da mahaifi, abin da wasu ke ganin ruwa ba ya tsami banza, kuma dalilin kishi ba zai sa uwa ta hallaka 'ya'yanta ba, don haka mutane ke fatan samun takamemen amsa duk lokacin da aka samu matar da ake zargi aka kuma gudanar da bincike.