Hotunan yadda mata ke caɓa kwalliya da jakar ledar Ghana Must Go

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

    • Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Mai ɗaukar hoto a Najeriya Obinna Obioma na amfani da wata hanya ta nuna yadda ake ado a Yammacin Afrika dan nuna tarihin ci rani da aka yi a baya.

Short presentational grey line

Jakar da ta yi fice da nau'in shuɗi da fari ko kuma ja da fari, wannan jaka da ba ta da suna ta daɗe musamman a kasuwannin Yammacin Afrika.

Amma a shekarun 1980 lokacin da dubban 'yan ciranin mafi yawansu daga Ghana suka bazu a Najeriya, sai ƙasar ta basu wani wa'adin da bai taka kara ya karya ba na cewa subar ƙasar, bayan sun fara amfani da ita ne suna zuba kayansu sai aka yi mata suna Ghana Must Go.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, OBINNA OBIOMA

Jaka ce mai sauƙin sha'ani da za a iya naɗe ta a sanya a aljihu, kuma tana da damar ɗaukar kaya masu yawa, wannan jaka ta taimaka wa mutan Ghana lokacin da suke komawa kasarsu.

Tun daga wannan lokacin aka daina kiranta da wani suna, a kasuwa ana kiranta Ghana Must Go - ana amfani da wannan jakar a Ghana, duk da cewa akwai raɗaɗin zafin da tarihin da jakar ke tunawa.

"Ina tuna lokacin da na ke tambayar iyayena da sauran 'yan uwana kan asalin jakar, yaya aka yi aka raɗa mata suna mai kyau," in ji Obinna da ke zaune a New York.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line
Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line

Tare da Chioma Obiegbu wata 'yar Najeriya da ke kwalliya da ke zaune a New York, da kuma Wuraola Oladapo mai ɗinki, sun ƙirƙiri wannan kaya tare da Obinna da suka fito da su ka a matsayin kayan kwalliya da ake amfani da su a arewaci da kuma kayan kwalliyar Afrika.

"A cikin kayan da aka ɗinka guda biyu, rigar saman an yi ta ne daga irin adon da ake yi a arewaci yayin da shi kuma siket an yi shi kamar yadda ake ɗaura zani a Yammacin Afrika.

"Akai kuma dan kwalin wanda aka dinka shi kamar yadda ake yi a Afrika. ya ce.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line
Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line

"Jakankunan ba suna nufin ci rani ba ne da ma'anar kalma domin nuna tafiya daga ƙasa zuwa ƙasa - in ji Obinna.

Matashin da aka haifa a Najeriya, ya fara zama mai ɗaukar hoto bayan sha'awar aikin da mahaifinsa ke yi, wanda ke daukar hotunan iyalai lokacin da suka fita yawo da kuma bikin kara shekara.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line

Amma ya fara samun kyamara ne daga wurin mahaifiyarsa bayan ya dawo daga makaranta a Burtaniya, yana banbanta aikinsa da na sauran mutane duk tsawon wannan shekaru na zamansa a Turai.

"Na samu kaina cikin yanayin ɗaukar hoto ina kuma bayar da labarin halin da mutane ke ciki ta hanyar. musamman wajen bayyana asalin mutane, al'ada da kuma abu buwan da aka gada a Afrika" in ji shi.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line

Jakar Ghana Must Go ta fuskanci abubuwa da dama, ciki har da haramta amfani da ita da jiragen KLM da Na faransa suka yi.

Har yanzu kuma haramcin na aiki, duk da cewa hukumomi a Ghana yi alawadai da hakan tare da bayyana shi a matsayin zagi da kuma nuna wariya ga 'yan Afrika da suke yawan amfani da ita wajen tafiya.

Haka zalika ana amfani da jakar a Najeriya, inda 'yan siyasa ke amfani da ita wajen karbar garin kuɗi na cin hanci, musamman yayin zaɓe. Akwai wannan ƙaurin sunan da ta yi, duk da cewa an samu ci gaba yanzu an daina ɗaukar garin kuɗin.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line

Amma jakar ta yi matuƙar shahara a faɗin Yammacin Afrika kuma yanzu akwai na'uka daban-daban da kuma girmanta.

Kuma har yanzu tana da araha, ga faɗi na daukar kaya da dama.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna Obioma

1px transparent line

Har yanzu Obinna na tunanin ko za a zo lokacin da za a daina amfani da ita.

"Na yi amannar Ghana Must Go za a ci gaba da kallonta a matsayin cin mutunci ga 'yan ƙasar Ghana.

"This begs to ask the question, should the name be changed, or the bags discontinued?" he asked.

"Wannan jakar na bayar da ayar tambaya ken cewa za a sauya mata suna ne ko kuma za a daina amfani da ita ne?" yake tambaya.

Model in Ghana Must Go fabrics

Asalin hoton, Obinna

1px transparent line