Bincike ya bankaɗo yadda sojojin Australia suka kashe fararen hula a Afghanistan

Unidentified Australian soldier

Asalin hoton, Getty Images

Wani rahoto da aka jima ana jira ya fitar da ƙwararan shaidu da suka nuna yadda sojojin ƙasar Australia suka kashe fararen hula 39 ba bisa ƙa'ida ba yayin yaƙin Afghanistan.

Ma'aikatar tsaro ta Australia ce ta fitar da sakamakon binciken da ta kwashe kusan shekara hudu tana yi game da yadda dakarunta suka aikata laifukan yaƙi.

A cewar rahoton akwai sojoji 19 da 'yan sanda za su yi bincike a kansu, kan kisan " 'yan gidan yari da manoma da kuma fararen hula" tsakanin 2009 da 2013.

Ma'aikatar tsaron ta dora alhakin wannan laifi kan halayyar ko-in-kula da wasu soji ke nunawa ga abokan aikinsu.

Binciken - wanda Manjo Janar Paul Brereton ya jagoranta - an gudanar da shi ne gaban sama da mutum 400 kuma ya gano cewa:

  • An umarci ƙananan sojoji da su fara yin kisa a karon farko ta hanyar kashe wasu 'yan gidan yari.
  • An binne makamai da wasu abubuwan fashewa kusa da wasu manyan gine-gine a Afghanistan saboda su ɓatar da waɗannan laifuka.
  • Ƙarin wasu abubuwa biyu da suka faru sun tabbatar da an aikata laifukan yaƙi.

Afghanistan ta ce ta samu tabbaci daga Australia cewa ta gudanar da wannan bincike ne domin tabbatar da adalci.

Samantha Crompvoets, wadda malamar makaranta ce kuma ita ce ta jagoranci bincike kan zarge-zargen, ta ce an yi wannan abin ne "da gangan kuma an maimaita ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba kawai domin a aikata laifin yaƙi". Ta ce ta gamsu da rahoton.

Me wannan rahoton ya gano?

Ya gano cewa akwai dakaru na musamman guda 25 da su ma suke da hannu cikin wannan kisa kai-tsaye ko kuma ta wasu hanyoyi na daban, a rikici 23 da aka yi a wurare daban-daban.

Shugaban ma'aikatar tsaron Janar Angus Cambell ya ce "babu wani abu daga cikin abubuwan da suka faru da za a kira kuskure".

Ya kuma bayyana wa manema labarai cewa, babu wani hari da aka kai ko kisa da aka yi da ke nuna cewa an yi su ne domin kare kai.

Janar Cambell ya ce sun samu shaida cewa dakaru na musamman suna da hannu cikin wannan kisa da aka yi ba bisa ka'ida ba.

Da farko an fara gudanar da binciken ne a boye, wanda yakan ya janyo samun bayanai da ba za su bayyana haƙiƙanin gaskiya ba, sai yanzu da aka gudanar da wannan.

Me ake cewa kan rahoton?

A makon jiya Mista Morrison ya yi gargadin cewa wannan rahoto na ƙunshe da wasu tsauraran bayanai da labarai masu tayar da hankali ga dakarun ƙasar na musamman.

Ofishin shugaban ƙasar Afghanistan Ashraf Ghani ya ce Mista Marrison ya kira su a waya tare da nuna rashin jin dadinsa game da abin da ya faru kan wannan binciken. Amma har yanzu Afghanistan ba ta ce komai ba game da rahoton.

Elaine Pearson ta kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta shaida wa BBC cewa: "Wannan wata hujja ce da ke nuna wadannan al'amura sun faru.

"Na yi matuƙar shan suka saboda kasancewa ta mace, farar hula, mai rajin kare hakkin mata, wani lokaci ma sai a ce ina neman mayar da aikina na mata," in ji ta.

"Ba wai ni ba ce kawai ban fahimci matsalar yaƙi ba," ta ƙara da cewa. Amma ya tabbata cewa akwai shaida an yi wasu gagaruman abubuwa da ba daidai ba."

Presentational grey line
Analysis box by Shaimaa Khalil, Australia correspondent

Me zai faru a nan gaba?

A makon jiya Mista Morrison ya ce akwai masu bincike na musannan da za a kawo domin gurfanar da wadanda suke da hannu a wannan badakala bayan da rahoton ya bayyana.

Kafafen yaɗa labarai na Australia na cewa binciken 'yan sanda kan batun zai iya ɗaukar shekaru kafin a gurfanar da su gaban mai shari'a.

Janar Campbell ya ce tuni aka rufe wani sashe ma'aikatan, kuma dole ne ma'aikatar tsaro ta daidaita abubuwa.

Shin an zargi wasu sauran ƙasashe kan wannan batun?

A farkon wannan shekarar ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta fara bincike kan zarge-zargen laifukan yaƙin da Amurka da sauran kasashen suka aikata a yaƙin Afghanistan.

Ana fatan bibiyar abubuwan da mayaƙan Taliban da dakarun gwamnatin Afghanistan da kuma sojin Amurka suka yi tun daga 2003.

Wani rahoton ICC a 2016 ya bankaɗo yadda sojojin Amurka suka riƙa azabtar da mutane a wani wuri na daban da CIA ke tafiyarwa.

Rahoton ya kuma nuna yadda gwamnatin Afghanistan ta riƙa azabtar da fursunoni da 'yan Taliban wanda kuma hakan laifin yaƙi ne, ciki har da yadda aka riƙa kashe fararen hula.