Ibrahim Maishunku ya tsallake rijiya da baya a wajen ƴan fashi a hanyar Kaduna-Abuja

Ibrahim Maishunku

Asalin hoton, @maishunku

Lokacin karatu: Minti 1

Fittacen jarumin fina-finan Kannywood Ibrahim Maishunku ya ce ya tsallake rijiya da baya a hannun ƴan fashi masu satar mutane.

Jarumin ya bayyana halin da ya shiga da shi da wasu abokanansa a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa a makon da ya gabata sun gamu da ɓarayi a kan hanyarsu daga Abuja zuwa Kaduna.

Maishunku ya ce ɓarayin sun shafe minti 30 suna ɓarin wuta inda suka kashe mutum 10 tare da yin awon gaba da mutum 15.

"Sun kuma yi awon gaba da abokina kuma ɗan uwa Abdullahi Abubakar Wali shugaban ƙungiyar matasa ta NYO," in ji shi.

Jarumin ya ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 7:16 na dare.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Kafin sanar da abin da ya faru da shi, Maishunku ya jefa mabiyansa cikin shakku bayan ya wallafa hoto a Instagram da ke nuna alamun tashin hankali tare da rubuta "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."

Amma a saƙon da ya wallafa daga baya ya ce bai yi niyyar faɗin abin da ya same shi ba. "Amma dole na fada domin neman addu'ar ƴan uwa," a cewarsa.

Jarumin ya yi wa abokinsa addu'ar Allah ya kuɓutar da shi tare da cewa ɓarayin sun buƙaci a biya su kuɗi.

Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta shahara sosai wajen fama da matsalar tsaro na satar mutane don neman kuɗn fansa.