Hotunan auren Bashir El-rufai sun tayar da ƙura a shafukan sada zumunta

Asalin hoton, Twitter- Bashir Elrufai
Bashir El-rufai, ɗa ga gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba ya neman shawara ga mutane kan yadda zai gudanar da rayuwarsa bayan hotunan baikonsa sun tayar da ƙura a shafukan sada zumunta.
A yammacin ranar Talata ne Bashir ya wallafa hotunan gabanin aure da masoyiyarsa Halima Kazaure, 'yar gidan tsohon minista a Najeriya, Ambasada Ibrahim Kazaure.
Za a ɗaura auren Bashir El-Rufai da Halima Kazaure ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.
Hotunan sun nuna su a jikin juna lamarin da ya jawo musu suka daga masu amfani da shafukan sada zumunta a kasar.
Galibin masu sukarsu suna cewa abin da suka yi ya saɓa wa addinin Musulunci saboda yadda suka rungumi juna.
Wani mai amfani da Twitter, mai suna Except Rasullilah, ya ce Bashir El-Rufai "Musulmi ne ɗan uwanmu, don haka a tunaninmu za mu wayar masa da kai kada ya fanɗare."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi kuwa Abdulhamid Abubakar ya ce: "Idan ka ga mutum yana sabon Allah hankalinsa kwance, hakan na alamta shaiɗan ya ci nasara akan sa."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Sai dai ba duka ne aka taru aka zama ɗaya ba domin kuwa wasu sun yi ta taya shi murna.
"Ina taya ka murna kai da Halima. Ba a hana mutane yin magana domin kuwa sai sun samu dalilin nuna kiyayyarsu, ba za ka taɓa yin daidai ba a wannan duniyar don haka ka yi kawai abin da zai sanya ka farin ciki," a cewar wani.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Shi ma Sulaiman fatan alheri ya yi wa Bashir da Halima yana mai cewa: "Allah Ya sanya alkhairi."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Raddin da Bashir El-Rufai ya mayar

Asalin hoton, Twitter/@BashirElRufai
A martanin da ya mayar kan masu tsokaci kan hotunan shirin ɗaurin aurensa, Bashir El-Rufai, ya caccaki waɗanda ba su ji daɗin yadda ya rike yarinyar da zai saura ba.
"Idan hotunan da na ɗauka da matata ba su yi muku daɗi ba da kuma yadda kuma yi tsokacin da ba a nema daga wurinku ba, ina son yin amfani da wannan dama domin cewa wannan abin da ya shafe ku ne.
Idan akwai wata hanya da za ta sanya waɗannan hotunan su kara ɓata muku rai don Allah ku gaya min," in ji shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5

Asalin hoton, Twitter/@BashirElRufai