Fatima Ribadu ta nemi afuwa kan kwalliyar bikin aurenta da ta janyo ce-ce-ku-ce

Malam Nuhu Ribadu da yarsa Fatima

Asalin hoton, @NuhuRibadu

Fatima Nuhu Ribadu ta nemi afuwa kan tufafin da ta sa a ranar ɗaurin aurenta da suka janyo cece-kuce musamman a shafukan sada zumunta na intanet.

A ranar Asabar ne aka ɗaura wa Fatima Ribadu, ƴar Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC aure da Aliyu Atiku Abubakar ɗan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar.

Hotunan auren sun ta yawo a shafunan intanet na sadarwa, saboda ƴaƴan manyan ƴan siyasa ne a Najeriya.

Sai dai kwalliyar da ƴar gidan Ribadu ta yi a ranar ɗaurin auren ce ta janyo ce-ce-ku-ce musamman farin tufafin da ta sa da wasu ke ganin sun nuna tsaraicinta.

A cikin saƙon da ta wallafa a Instagram, Fatima Ribadu ta ce ta yi nadama kan yadda hotunan suka fita shafukan sada zumunta ba da son ranta ba.

"Ina neman afuwa ga abokai da dangina bisa wannan kuskuren," in ji ta.

Ta ce yanayin rigar da ta saka ne ke nuna kamar jikinta, "Ba zan taɓa yin haka ba," a cewarta.

Ta gode wa dukkanin waɗanda suka kare ta kuma yi mata kallon fahimta.

Sakon Fatima Ribadu

Auren ya samu halartar manyan jiga-jigan ƴan siyasa a Najeriya daga manyan jam'iyyun siyasar ƙasar APC da PDP da suka ƙunshi jagororin jam'iyyun da kuma gwamnoni da ministoci da sauran manyan ƴan siyasa.

Wasu na ganin bai kamata ta yi irin shigar da ta yi ba musamman kuma yadda aka ga hotunanta cikin manyan mutane da suka haɗa da gwamnoni da abokanan mahaifinta da manyan ƴan siyasa a Najeriya.

Fatima Nuhu Ribadu da angonta Aliyu Atiku Abubakar ranar ɗaurin aurensu

Asalin hoton, @TMZNaijaCeleb

Bayanan hoto, Fatima Nuhu Ribadu da angonta Aliyu Atiku Abubakar ranar ɗaurin aurensu