A Makon Jiya a Najeriya: An yi wa 'yan Najeriya ɗaurin rai-da-rai a Abu Dhabi, an kori 'yan sanda 17 daga aiki

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya ko kuma ga 'yan Najeriya a makon da ya gabata daga Lahadi, 8 zuwa Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2020.

An yanke wa 'yan Najeriya hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan alaƙa da Boko Haram a Dubai

..

Asalin hoton, AFP

A makon da ya gabata ne aka samu rahoton cewa wata kotu a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yanke wa wasu 'yan Najeriya shida hukunci kan alaƙarsu da ƙungiyar Boko Haram.

An zarge su ne da ɗaukar nauyin ƙungiyar ta Boko Haram ta hanyar ba su kuɗaɗe.

Kotun daukaka ƙarar da ke zama a Abu Dhabi ta kama mutum shidan ne da laifin taimaka wa ƙungiyar Boko Haram da kuɗi, ta hanyar tattara mata kuɗi daga kasashen waje, tana haɗa baki da wasu masu sana'ar canjin kudi a Najeriya.

Kotun ta raba mutunen ne gida biyu, kashi na farko na mutum biyu da ta yi musu hukunci ma fi tsanani, bayan ta dogara da binciken da ta yi, wanda ya kawar mata da dukkan shakku cewa ƴan Boko Haram ne.

Yayin da kashi na biyu kuma mai mutum huɗu, ta yi musu hukunci mai sassauci - na ɗaurin shekara 10, saboda fahimtar ba su shiga ƙungiyar har wuya ba.

Abdulkadir Balarabe Musa: Tsohon gwamnan Jihar Kaduna ya rasu

..

Asalin hoton, OTHER

A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna da ke Najeriya Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu.

Ya rasu ne a birnin Kaduna yana da shekara 84 a duniya.

An yi jana'izarsa da misalin karfe huɗu agogon Najeriya a Masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna.

Marigayin na cikin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka taka rawa wajen tabbatar da mulkin dimokradiyya.

Ya zama gwamna ne 1979 a karkashin jam'iyyar PRP, ko da yake an tsige shi a 1981 kafin ya kammala wa'adinsa.

Baligai a jihar Kaduna za su fara biyan N1,000 a matsayin haraji

..

Asalin hoton, KSGH

A wannan makon ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ƙara ɗabbaƙa dokar nan da aka daɗe ba a amfani da ita ta kowane baligi ya biya haraji.

Shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Dr Zaid Abubakar wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da kuɗin ne wajen gina jihar.

Hukumar ta ce wajibi ne ga duk wanda ya haura shekara 18 ya riƙa biyan naira 1,000 duk shekara a matsayin haraji.

Jama'ar jihar da dama sun yi maraba da wanna mataki na jihar, wasu kuma suka nuna ɓacin ransu kan wannan mataki inda suka danganta shi da zalunci.

An sallami 'yan sandan Najeriya 17 an rage wa 18 muƙami

..

Asalin hoton, Nigeria Police

A ranar Alhamis ne rundunar ƴan sanda a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta sallami jami'anta goma sha baƙwai da kuma bai wa wasu da dama takardun gargaɗi da kuma horo na gwale-gwale.

An samu ƴan sandan da aikata ba daidai ba da suka haɗa da kisan kai da kuma wuce gona da iri.

Sanarwar da rundunar ƴan sanda ta jihar Legas ta fitar wadda ta aike wa BBC, ta ce wannan mataki da ta ɗauka, wani ƙoƙari ne na inganta tarbiyya da kyawawan ɗabi'u na ƴan sanda a jihar Legas.

Rundunar ta yi wa ma'aikata 81 shari'a kan laifuka daban-daban na ladabtarwa da suka aikata tsakanin watan Oktoba na shekarar 2019 da watan Oktoba na shekarar 2020, ciki kuwa har da sallamar ƴan sanda 17 daga bakin aiki, bayan an same su da aikata ba dai-dai ba.

An ƙara kuɗin mai a Najeriya

..

Ƴan Najeriya sun wayi garin Juma'a da labarin ƙarin farashin man fetur inda akasari gidajen man suka fara sayar da man a sabon farashin naira 170.

Shugaban ƙungiyar manyan dillalan man fetur na arewa maso yamma da wasu jihohi, Bashir Ɗanmalam ya shaida wa BBC cewa gidajen mai za su fara sayar da man fetur tsakanin naira 168 zuwa 170, saɓannin 158-160 da ake sayarwa a baya.

Hukumar ƙayyade farashin man fetur ta Najeriya wato PPMC ce ta ƙara kuɗin man fetur a depo-depo zuwa 155.17.