'Da ihu muke yaƙar giwayen da ke kawo farmaki garinmu'

A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyam wasu mazauna garin Rann a yankin karamar hukumar Kala Balge, na kokawa da iftila'in farmakin da wani garken giwaye ke kai musu,
Giwayen dai na barnata amfanin gonakinsu inda a wasu lokuta ma su kan yi ƙoƙarin shiga cikin gari.
Bayanai dai sun nuna cewa giwayen na shigowa garin ne daga ƙasar Kamaru mai maƙwabtaka kuma sun fi shiga ne a cikin dare.
Hukumomin jihar ta Bornon dai sun ce za su tattauna da gwamnatin Kamaru don shawo kan matsalar farmakin giwayen, baya ga matakin da ta ce za ta ɗauka wajen tallafawa wadanda ɓarnar ta shafa.
Matsalar farmakin giwaye a gonaki da kuma gidaje abu ne da aka shafe shekaru ana fama da ita a wasu yankunan jihar Borno, musamman ma wadanda ke kusa da kan iyakoki ƙasashen Kamaru da Chadi, inda bayanai ke nuna cewa galibi garken giwayen kan bullo ne daga wadannan ƙasashe a duk shekara.
Ɗaya daga cikin manoman garin Rann ya shaida wa BBC cewa, giwayen na kai musu farmakin ne a kai - a kai.
"Sai da mu ka riga suka sakankance cewa giwayen ba za su sake dawowa a kusa ba, bayan barnar da suka tafka mana a watannin baya, sai gashi sun kawo musu sabon samame cikin dare."
'Ihu na taimaka mana wajen fatattakar giwaye'
Mutanen garin Rann ba su yi kasa a gwiwa ba wajen nema wa kan su mafita ta wucin gadi don kaucewa yawan kai farmakin giwayen inda su kan taru yaransu da manya idan giwayen sun kai farmakin sai su zagaye su suna yi musu ihu saboda ita giwa a rayuwarta bata son ihu ko hayaniya.
Ihun da mutanen garin ke yi ne kansa giwayen koda sun nufi kofar shiga garin sai su juya su koma inda suka fito.
Me gwamnati ke cewa?
Mai bai wa gwamnatn jihar Borno shawara kan harkokin gine-gine, kuma tsohon shugaban karamar hukumar ta Kala Balge, Zanna Abubakar Jabu, ya shaida wa BBC irin kokarin da gwamnatin ke yi wajen daƙile farmakin giwayen.
Sannan ya ce gwamnatin jaharsu za ta tuntuɓi gwamnatin Kamaru inda suke kyautata zaton daga nan giwayen suke fitowa wajen tattaunawa yadda za a shawo kan wannan farmaki.
Karin haske
Da ma dai tun a shekarun baya al'umomin irin wadannan yankunan jihar musamman garin Izge da ke karamar hukumar Gwoza da wasu yankunan da ke kusa da su suka rika fama da farmakin giwaye, inda sukan lalata amfanin gona.
Abin da wasu masana ke cewa hakan baya rasa nasaba da maƙwabtakar da wadannan yankuna suke yi da ƙasar Kamaru inda aka bayyana ta nan ne giwayen kan taso har su dangana ta cikin dazuka su bullar har zuwa jihar Yobe mai makwabtaka da jihar Borno.










