Ranar Giwaye Ta Duniya: Matar da ke ƙoƙarin ceto giwayen da ake azabtarwa a Indiya

Asalin hoton, Sangita Iyer
- Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Sama da shekaru bakwai, Sangita Iyer na fafutikar kawo karshen cin zarafin da ake yi wa giwaye da sunan addinai.
''Wani Ubangijin ne zai amince da irin wannan cin zalin akan abin da ya halitta? Abin na tattarre da takaici,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.
Mawallafiyar an haife ta a jihar Kerala ta India ( yanzu haka tana zama a Toronto), kuma dai kamar galibin yara, ita ma ta taba kasancewa mai sha'awar giwaye.
''Na kan iske yadda giwaye ke kai komo abin sha'awa a lokacin da nake yarinya suna burgeni domin ina ganin kyansu,'' a cewar Sangita Iyer.
Sai dai daga baya ta fahimci irin mawuyancin hali da dabbar ke ciki.
Munanan rauninka
Bayan shafe tsawon shekaru a Canada, ta koma Indiya a 2013 a karon farko domin halarta taron addu'ar cika shekara daya da rasuwar mahaifinta.

Asalin hoton, Sangita Iyer
A lokacin balaguron, Sangita ta gamu da giwaye a hanya amma ba sa sanye da kayan kwalliyar da masu bauta ke sanya masu don ado. Abin ya bata mamaki.
"Da dama daga cikin giwayen akwai rauni a kugunsu, an azabtar dasu ga jini ta ko ina, an sanya ankwa ta hanyar huda kafarsu - su na ta zub da jini."
Labarin Sangita, Abin bauta a cikin ankwa, ya bankado irin wahalar da giwaye ke ciki.
"Suna cikin yanayi na galabaita, sannan ankwa da aka sa musu masu nauyi ne. Abin ya sosa mun rai ganin yanayin da suke ciki."
Martaba
Addinin Hindu da Budda na girmama giwaye da martaba. Tsawon shekaru, wurare ko gine-ginen ibadu ana bauta musu. Da neman biyan bukatu da albarka.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai darajar giwayen na raguwa sosai a duniya tun kafin mutuwarsu.
A kusa da Kerala akwai fitaccen wurin bauta da ake kira Guruvayur, an kera gunkin wani giwa da ya yi fice mai suna Kesavan. Haurensu ake soma hangowa a kofar shiga gini.
Munafunci
Akwai bayanai da ke cewa Kesavan ya zagaye ginin wurin bautar kafin ya fadi ya mutu a 1976, yana da shekara 72.
Ba bakon abu ne ganin yadda mutane suke taruwa a ginin wurin bauta suna makokin mutuwa giwaye - ko da ba fitattu ba ne.

Asalin hoton, Sangita Iyer
"Suna azabtar da giwayen har mutuwa, sannan bayan sun mutu sai su rinka kukan karya, kamar da gaske abin ya sosa ran su,'' a cewar Sangita.
Ta bayyana kan ta a matsayin kabilar Hindu da ke adawa da kawo karshen wuraren da ake bauta wa giwaye.
Indiya ta cafke giwaye 2,500, wanda kaso mafi yawa a yankin Kerala suke. Mallakin wuraren bauta ne da kuma daidakun mutane.
Sangita ta fahimci tambarin al'adu da addinai a kan giwaye.
Amma a matsayinta na mai digiri a fanin nazarin halitta da muhalli ta san cewa giwaye na da basira, tausayi da son walwala a cikin dabobbi, suna jure tafiya mai nisa a jeji domin neman abinci da ruwa.
Rayuwarsu
Kafafuwansu basa jure tafiya akan siminti mai kankare da kuma hanyoyin da aka samar da duwatsu, saboda zafi.

Asalin hoton, Sangita Iyer
Sautin kida idan ya yi yawa na harzuka su haka nan hayaniya da taro da wasan tartsatsin wuta, da ake yi lokacin bukukuwa.
"Wadannan daba ana gallaza musu ta hanyar amfani da karafa masu kaifi wajen huda sassan jikinsu, sanya musu kaca ko ankwa a kafafu, suna shiga cikin azaba da radadi,'' a cewar Sangita.
Cutarwa
A lokacin da take tattara bayananta da bincike tayi kokarin nadan bidiyo na tsawon sa'o'i 25 da adana wasu bayanai na cin zarafi.

Asalin hoton, Sangita Iyer
"Na kadu zuciyata ta shiga radadi. Na fadawa kai na ba zan iya juya wa wadannan kyawawan dabobbi baya ba."
Ta shiga yanayi na rauni, muryata ta karaya a lokacin da take bada bayani da misalai na tsantsan mugunta da rashin Imani da aka aikata akan wani giwa da ake kira Ramabadran, mallakin mahukunta wurin bauta Thiruvambadi.
"Abin takaici ne ganin yadda wannan giwa ke kokarin amfani da hancinsa da ke karye wajen shan ruwa a cikin tanki. Ya kasa zukar ruwa.''
Yanayinsa ya yi tsanani domin hukumar kula da lafiyar dabobbi ta Indiya ta shawarci a yi masa mutuwar hutu. Amma hakan aka ci gaba da amfani da shi a bukukuwan bauta har rai ya yi halinsa.
Tsiyayar jini
Akwai giwar da aka iske ciwonsa ya yi ruwa yana tsiyayowa.

Asalin hoton, Sangita Iyer
"Kacar da aka saka wa giwar ta ci jikinsa har jinni na tsiyaya. Na rasa gane yadda mutane ke iya aikata hakan?"
Masu kula da giwayen na gana musu azaba, amma masu giwayen basu damu ba, su dai kawai a samu kudi ko riba.
Kasuwanci
"Kungiyar da ke harkar giwaye na samun kudi sosai.vWasu giwayen na samar da kudin na yawansu kan kai dala dubu 10 a lokacin bukukuwa."
Thechikkottukavu Ramachandran daya daga cikin giwan da ke samar da makudan kudade kenan.
Ana bayyana shi a matsayin mafi girma a Asia. Yana jan hankali sosai domin mutane na fatan tozali da shi a duk lokacin da ake taron tattakin giwaye na shekara-shekara a Thrissur, haka kuma shafin Wikipidea na yawan Magana akan giwan
Yanzu Ramachandran na da shekara 56 kuma baya gani sosai. Ya sha tafka ta'adi saboda gajiyar da shi da ake yi sannan ya kashe akalla mutum 6.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai har yanzu kokarin da hukumomin masu kula da dabobbi ke yi na ganin an masa ritaya daga irin wannan ayyukan na fuskantar turjiya.
Har yanzu ana shiga da shi taron jama'a
"Wadannan giwaye ba wai an halice su ba ne domin biyan bukatun bil adama,'' a cewar Sangita.
Ta ce ana kirkiro bukukuwa domin samun kudi da giwaye. A cikin giwayen, mahukunta Kerala sun fi son Namijin giwa, yayin da su kuma matan aka fi amfani da su a kudancin Indiya.
Soyayya
A 2014, Sangita ta shaidi yadda aka turke wata giwa wanda hakan ya janye hankalinta baki daya. "Lokacin dana soma ganin Lakshmi, ta tafi da Imani na nan take."

Asalin hoton, Sangita Iyer
"Na taba ta. Na sa hannu na a kasan wuyanta na shafo kirjinta. Nan take kuwa ta zuro mun hancinta ya taba hannu na ta shinshina ni. Jikinta abin lalabawa ne a gare ni.''
Sangita ta debo ruwa a tafin hannuta sannan ta rinka bata abarba da ayaba. Nan take aka samu shakuwa. Bayan shekara guda ta kadu bayan sake haduwa da Lakshmi.
"Na shiga hali na dimauta lokacin dana ga kwalla a idanunta. Tana amfani da hancinta tana goga jikinta da yiwa kanta tausa.''
Cin zali
Lakshimi ta dau abinci wanda yake kula da ita don haka a fusace ya ci zarafinta ba tare da tunanin yi mata afuwa ba.

Asalin hoton, Sangita Iyer
Tsumagiyar da ya yi amfani da shi wajen dukanta ta sauka akan idonta, don haka ta makance.
"Kyawawan idanun Lakshmi sun juye sun koma wani iri. Wannan misali ne guda na irin cin zarafi da azaba da ake yi wa dabobbi.'' Sangita na da yakinin Lakshmi ta aikata hakan ne saboda yunwa.
''A wurin bauta ba a bai wa giwaye abinci, saboda ana fargabar za su yi kashi a cikin wurin.''
Sangita ta shigar da korafi da kuma sanadin korar mai kula da giwar. Hakan ya sake ta'azzara yanayin da Lakshmi ke ciki.
Rashin amfani
A kokarin tabbatar da cewa giwaye sun bi umarni masu kula dasu, akan jefa su cikin yanayi ko ayukan azabatarwa.

Asalin hoton, Sangita Iyer
Namijin giwa da aka cafke na fuskantar cin zarafi da sunan horo.
"Ana daure su sannan ayi musu dukan tsiya na tsawon sa'a 72 ko har zuwa lokacin da za su saduda da bin duk wani umarni."
"Suna komawa kamar wawaye domin amfaninsu ya kare. Akasarin giwaye na rayuwa ne kamar kwarangwal. Yanayin akwai wahalarwa."
Haramci da tilastawa
A kasashe masu kabilar Budda kamar Sri Lanka da Thailand, ana amfani da giwaye wajen bukukuwan addinai iri guda.

Sangita ta bayyana fargabar yadda bukatar hakan zai tilasta cigaba da kame wadannan dabobbi ta haramtaciyar hanya, kamar yadda wasu rahotanni a shekarun baya daga Sri Lanka suka shaida.

Asalin hoton, Sangita Iyer
Kokenmu
Ta fuskanci barazana daga mutane da suka nada kansu a matsayin masu kare al'adu.
"Ana cin zarafi na a shafukan sada zumunta. Mu (masu fafutika) ana mana kallon marasa kan gado
"Amma idan suna tunanin za su rufe mana baki ta hanyar cin zarafi, sun yi babban kuskure. Muryoyinmu da kokenmu yanzu aka soma jinsu a wannan lokaci ma da babbar murya."

Asalin hoton, Sangita Iyer











