Giwa ta kashe mafarauci sannan zaki ya cinye shi

zaki ya cinye mafarauci bayan da giwa ta halaka shi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zaki ya cinye mafarauci bayan da giwa ta halaka shi

Giwa ta hallaka wani da ake zaton mafarauci ne, sannan kuma wani garken zakuna ya yi kalaci da shi a gandun dajin Kruger National Park da ke kasar Afirka Ta Kudu.

Abokin tafiyar mafaraucin ne ya shaida wa iyalansa cewa giwa ta hallaka shi ranar Talata. Daga nan ne kuma 'yan uwansa suka shaida wa masu kula da gandun dajin.

A ranar Alhamis ne aka tsinci riga da wandonsa da kuma kasusuwansa a gefe guda a kokarin da ake yi na samo gawarsa.

Hukumar da ke kula da gandun dajin dai ta mika sakon jajantawa ga iyalan mafaraucin.

Haka kuma hukumar ta gargadi masu shiga dajin da kafa cewa yin hakan yana da matukar hadari ga rayuwarsu, kuma wannan lamari da ya faru hujja ce a kan hakan.

Gandun dajin dai na fama da matsalar karuwar mafarauta a cikinsa wadanda ke shiga dajin domin nema kahon bauna, saboda tsananin bukatarsa da ake yi a kasashen Asiya.

Ko a ranar Asabar din da ta gabata ma dai , mahukunta a filin jirgin saman Hong Kong sun kwace wani kahon bauna mafi girma da aka taba gani a cikin shekara biyar, wanda kuma darajarsa ta kai dala miliyan biyu da rabi.