Obama ya caccaki Trump kan rashin taɓuka abin arziki

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya soki Donald Trump a jawabinsa na farko da ya yi a wajen kamfen din nuna goyon-baya ga ɗan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democrats, Joe Biden.
A jawabin da ya gabatar a Philadelphia, Mista Obama ya ce mista Trump ya rike mulkin ƙasa kamar shirin talabijin.
Sannan ya kuma zargi shugaban da zuki tammale a koda yaushe da kuma caccakarsa kan yadda ya tunkari annobar korona.
Mista Obama, ya ce "Ban taɓa tunani Donald Trump zai yi watsi da tsare-tsaren da na ɗora ƙasa a kai ba ko kuma ci gaba da manufofina ba, amma dai na yi zaton ko saboda darajar ƙasar zai iya nuna wata sha'awa ta daukar aikinsa da muhimmanci".
Ya ce, To sai gashi hakan bai samu ba ma'ana bai ɗauki aikin da muhimmanci ba sai dai kawai ya taimaka wa kansa da kuma na kusa da shi.
Tsohon shugaban na Amurka ya kuma yadda Trump ya ɗauki aikinsa tamkar shirin talbijin ne da zai iya amfani da shi wajen jan hankalin jama'a, amma ba haka abin yake ba domin shi mulki ba shiri ne na talbijin ba, abu ne da zaka dauka da muhimmanci.
Yanzu aƙalla Amurkawa dubu 220 ne suka mutu, yayin da aka rufe kananan masana'antu fiye da dubu 100, haka mutane da dama sun rasa ayyukansu gashi kimar Amurka a ƙasashen duniya ta ragu inji Obama.
Shima a yayin da ke yaƙin neman zabe a North Carolina, Donald Trump ya ce Mista Obama ya yi wa Hilary Clinton yaƙin neman zaɓe amma daga ƙarshe me ya biyo baya ai faduwa tayi.
Ya ce zaɓen Amurka a yanzu zai kasance ne tsakanin Trump wanda ya yi matukar farfaɗo da tattalin arziki da kuma Biden, wanda zai mayar da hannun agogo baya.










