Zaɓen Amurka na 2020: Me ya sa Trump ya raina wayon Afirka?

Donald Trump speaks with African flags in the background

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Nomsa Maseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Johannesburg

"Kwata-kwata Trump ya gama raina Afrika, bai taɓa ziyartarta ba tun da aka zaɓe shi, kuma ba na jin zai je ko da an zaɓe shi a karo na biyu,'' in ji Farfesa John Srremlu, wani malami da ke koyar da ilimin diflomasiyya a Jami'ar Witwatersrand da ke Afrika Ta Kudu.

Dukkanin shugabannin da suka gabace shi Barrack Obama da kuma George W Bush sun kai ziyara nahiyar a zangon farko na mulkinsu, amma Trump bai taɓa samun lokacin zuwa ba.

''Ya ɗauka cewa Afrika ba ta ishe shi kallo ba'' in ji Farfesan.

Ga mutane da dama, matakin na Trump, ya fito da matsayar gwamnatinsa a fili dangane da Afrika.

Alaƙar kasuwanci tsakanin Amurka da nahiyar ta yin tsami musamman a shekarun baya-bayan nan, duk da cewa ƙasashe da dama da tattalin arziƙinsu ke bunƙasa cikin gaggawa sun mayar da hankali kan kasashen da ke Kudu da Hamadar Sahara.

Da alama Washington ta watsar da Afrika musamman kan batutuwan da suka shafi bayar da agajin harkokin lafiya da dimflomasiyya.

'Bana iya samun maganin hana ɗaukar ciki'

Kimanin tafiyar sa'a biyu daga wajen babban birnin Lesotho, Maseru, ta ce ana jin tasirin wannan mataki.

Ko da yake ƙasar na daya daga cikin ƙasashen Afirka da dama da manufofin Amurka suka shafa, abin da ke faruwa a nan alama ce ta yadda shawarar Washington ta shafi nahiyar gaba ɗaya.

Tana kewaye da duwatsu tare da gidajen laka, an rufe wani asibiti guda ɗaya tak da ke ƙauyen Ha Mojela, an rufe ƙofofin asibitin, sannan makullinsa ya yi tsatsa.

An rufe asibitin saboda zaftare tallafin da Amurka take bayarwa a fannin lafiya
Bayanan hoto, An rufe asibitin saboda zaftare tallafin da Amurka take bayarwa a fannin lafiya

"Na kasance ina ziyartar asibitin a kowane wata don karɓar magungunan hana haihuwa amma yanzu an tilasta min saya saboda asibitin da na dogara da shi a rufe yake.

''Ba zan iya samun damar saya duk wata ba kuma ina jin tsoron zan yi ciki", in ji Malerato Nyai mai shekaru 36, mace siririya kuma mai kunya wacce ta yi murmushi.

Kalaman nata sun yi kama da na masu zuwa asibitin da dama. Ɗaya daga cikinsu ta bayyana fargabar cewa 'ya'yanta mata za su iya samun juna biyu saboda rashin samun magani a asibitin.

Malerato ta ce bata iya siyan maganin hana daukar ciki, sannan tana fargabar zata iya samunshi a nan gaba
Bayanan hoto, Malerato ta ce bata iya siyan maganin hana daukar ciki, sannan tana fargabar zata iya samunshi a nan gaba

Ana danganta ɗaukar matakiin da manufar Amurka wacce ke hana bayar da kuɗinta ga ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda ke taimaka wa mata wajen zubar da ciki.

An bijiro da manufar ne tun 1984, daga bisani kuma duk wani shugaban ƙasa na jam'iyyar Republican da ya hau kan mulki kan ɗabbaka ta.

Shugaba Donald Trump ne ya sake gabatar da ita a shekarar 2017.

Wannan yana nufin shawarar da aka yanke a Washington ta yi tasiri matuƙa ga yawancin matan Afirka da ke zaune a ƙasashen da suka dogara da taimakon ƙasashen waje.

Tlali Matela na taimakawa mata ta fuskar tsarin iyali a Lesotho
Bayanan hoto, Tlali Matela na taimaka wa mata ta fuskar tsarin iyali a Lesotho

Amma ba kawai rashin hana haihuwa ba ne ke damun mutane a ƙasashen Afirka da dama.

Rashin bayar da tallafin Amurka ya haifar da dakatar da gwajin HIV da binciken kansar mahaifa.

Tlali Matela ya ce "Lokacin da aka dakatar da tallafin lamarin ya janyo watsar da mutanen da suke ba su kulawa kan cutar ƙanjamau.

An fi jin tasirin matakin da gwamnatin Trump ta ɗauka na tsayar da tallafin a kasashen Kudu da Hamadar Sahara fiye da kowane yanki na duniya.

Dalili kuwa shi ne, yankin ya fi kowanne yawan masu kamuwa da cutar a duniya, sannan ta kasance babbar hanyar mutuwar mutane a yankin.

Sauyi manufar kasuwanci

Lamarin ba wai kawai ya shafi fannin kiwon lafiya ba ne. Dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da Afirka ta yi rauni.

Akwai fargabar ba za a sake sabunta Dokar Ci Gaban Afirka da aka fi sani da AGOA ba bayan 2025.

An sanya hannu kan dokar ne shekaru 20 da suka gabata, sannan ta bayar da dama ta musamman ga kasuwar Amurka don shigo da kaya daga kusan kasashe 40.

Yarjejeniyar ta AGOA ta taimaka wajen farfaɗo da masana'antun masaƙu a ƙasar Lesotho kuma sun ɗauki ma'aikata sama da 46,000, yawancinsu mata ne.

Rayuwar mutane da dama ta ta'allaka a kan tallafin da dangantakar kasuwanci da Amurka
Bayanan hoto, Rayuwar mutane da dama ta ta'allaka a kan tallafin da dangantakar kasuwanci da Amurka ke samarwa

Idan ba a sabunta yarjejeniyar ba dubban mutane na iya rasa aikinsu.

"Zai zama babban ibtila'i a gare mu duka. Ina fatan za a tsawaita ta saboda idan ta ƙare hakan na nufin za mu rufe baki dayanmu kuma mu zama marasa aikin yi kuma ba za mu iya yin gogayya da ƙasashen waje ba , "in ji David Chen, wani mai kamfanin masana'antun masaƙu na Taiwan wanda ke da ma'aikata 1,600 a Lesotho.

Mista Chen yana fitar da tufafin motsa jiki ne kawai zuwa Amurka.

Masana'antarsa ita ce mafi girma a masana'antu masu zaman kansu a ƙasar kuma ana iya ganin hakan ƙarara da zarar an shiga ciki.

Sa'o'in aiki a wajen na da yawa, amma mata ma'aikata suna aiki tuƙuru, suna fitar da dubban tufafi kowace rana duk da ƙarancin albashi, sannan dubban ɗaruruwan mutane sun dogara ne da aikin.

"Zai zama babban ibtila'i a garemu, " in ji David Chen
Bayanan hoto, "Zai zama babban ibtila'i a garemu, " in ji David Chen

Rashin ɗaukar Afrika da muhimmanci da Trump ke yi

Amurka ba ta kasance mai saka jari ba a ƙasashen Afrika. Wannan ya bar giɓi ga Indiya da Turkiyya, da Rasha da kuma China.

Sun yi amfani da wannan dama wajen haɓaka diflomasiyyarsu, da kasuwanci da saka jari a nahiyar.

Kamfanonin ƴan Chinaa ne ke samar da yawancin kayayyakin da ake amfani da su a nahiyar.

Mafi yawansu suna samun tallafi daga gwamnati a Beijing, sannan China na gina hanyoyin tashar jiragen ruwa da filayen jiragen sama a duk faɗin Afirka, hakan yana ƙara ƙarfafa kasancewarta a nahiyar.

Kasar Lesotho ta dogara sosai a kan kasuwanci da Amurka
Bayanan hoto, Kasar Lesotho ta dogara sosai a kan kasuwanci da Amurka

Alaƙar China da Afirka

China ta zama babbar mai faɗa a ji a Afirka tun kafin Shugaba Trump ya hau mulki.

Amma Beijing ta inganta tasirinta a nahiyar a lokacin gwamnatin Trump.

A wani kyakkyawan wuri da ke Kwarin Qacha's Nek, a ƙasar Lesotho, 'yan kilomitoci kaɗan daga iyakar Afirka Ta Kudu, wata shimfideɗiyar hanya ce da aka fara aikin samarwa shekara guda da ta gabata.

Bankin Exim na kasar China ne aikin samar da ita, sannan tana da tsawon kilomita 91 a kan dala miliyan 128.

Ana fatan samar da hanyar sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin gundumomi daga awanni huɗu zuwa biyu.

"Gina wannan titin zai bunƙasa yawon bude ido saboda ya hade da gandun daji na Sehlabathebe, wanda shi ne kaɗai kasar Lesotho da take da kayayyakin tarihi ke da shi", in ji Teboho Mokhoane, daraktan hukumar samar da hanyoyin ta Lesotho.

China na kara samun wajen zama a Afrika ta hanyar samar da tituna da iyakokin ruwa a dukkanin sassan Afrika
Bayanan hoto, China na kara samun wajen zama a Afrika ta hanyar samar da tituna da iyakokin ruwa a dukkanin sassan Afrika

Rikicin kasuwanci tsakanin Washington da Beijing na ƙara ƙamari.

Abin da kawai ya rage shi ne a ga yadda za ta kaya, duk da yake manufar Shugaba Trump ita ce "Amurka ta zama babba", amma gwamnatinsa ba ta damu da daya daga cikin yankuna masu saurin bunƙasa a duniya ba.

Abin jira a gani shi ne abin da sakamakon zaɓen na Amurka mai zuwa ke nufi ga Afirka.